Tirkashi: Tsohon Dan Majalisa na Shirin Ballo Aiki ga Atiku a Amurka
- Tsohon ɗan majalisar tarayya Ehiozuwa Agbonayinma ya aika wa Donald Trump takarda yana neman a sake duba tsohon binciken kuɗin da ya shafi Atiku
- Ya nemi hukumomin Amurka su sake nazarin bayanan binciken da aka gudanar tun 2006, da kuma rahoton wani kwamitin Majalisar Dattawan Amurka
- Agbonayinma ya jaddada cewa zarge-zargen da binciken suka ƙunsa ba sa nufin an tabbatar da cewa wani mutum ya aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja – Tsohon ɗan Majalisar Wakilan Najeriya kuma tsohon Kwamishinan Tarayya a hukumar CCB, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump kan Atiku Abubakar.
Tsohon dan majalisar ya roki Shugaba Trump da ya sake duba wani tsohon binciken kuɗi da ya shafi Atiku Abubakar.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Agbonayinma ya yi wannan buƙata ne a wata takarda mai ɗauke da ranar 24 ga Satumba, 2026, wadda aka rabawa manema labarai a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan
Amurka ta gode wa Birtaniya da wasu kasashen musulmi 3 kan goyon bayan yaki da Iran
Ya nemi a sake duba binciken da aka fara a 2006
Tsohon ɗan majalisar ya roƙi Trump da ya umarci hukumomin Amurka da abin ya shafa su sake nazarin binciken da aka fara sakamakon wata wasiƙa da Ofishin Babban Lauyan Amurka ya aika wa hukumomin Najeriya ranar 22 ga Yuni, 2006.
Ya ce wasiƙar na ɗauke da lambar MEW:DPW:KDL:AV 1 File 182-23818.
Agbonayinma ya kuma nemi a sake duba dukkan bayanan da suka shafi binciken, ciki har da takardun da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta samar bayan karɓar buƙatar daga Amurka.
An nemi a sake nazarin rahoton Majalisar Dattawa
Tsohon ɗan siyasar ya kuma buƙaci hukumomin Amurka su sake nazarin sakamakon binciken wani kwamitin Majalisar Dattawan Amurka da aka gudanar a zaman da aka yi ranar 4 ga Fabrairu, 2010.
Agbonayinma ya ce bayanan da ya ambata a cikin takardarsa sun ƙunshi zarge-zargen cin hanci, halatta kuɗin haram, damfara ta hanyar aika kuɗi ta yanar gizo, haɗa baki da kuma wasu harkokin kuɗi da ake dangantawa da wasu mutane da kamfanonin da ke da alaƙa da Atiku.
Sai dai ya jaddada cewa waɗannan zarge-zarge da sakamakon binciken ba su kamata a ɗauke su a matsayin hujjar cewa wani mutum ya aikata laifi ba.
“Wannan kira ba sanarwar cewa wani mutum yana aikata laifi ba ne, illa buƙatar hukumomin da suka dace su binciki bayanan tsohon binciken domin tantance ko akwai wani lamari da har yanzu doka za ta iya ɗaukar mataki a kansa,” in ji shi.
“Babu wanda ya fi ƙarfin doka”
Agbonayinma ya kare matakin da ya ɗauka, yana mai cewa manufarsa ita ce neman gaskiya da sanya hukumomi yin abin da ya dace, ba amfani da binciken wajen musgunawa wani mutum saboda siyasa ba.
“Babu wanda ya kamata ya fi ƙarfin doka. A bar hujja ta yi magana. A bar doka ta yi aikinta,” in ji shi.
Ya roƙi Trump da hukumomin Amurka da abin ya shafa su tantance ko bayanan tsohon binciken sun isa a sake ɗaukar wani mataki, yana mai cewa manufarsa ita ce a tabbatar da matsayin batun a gaban doka, ba yanke hukunci kan kowane mutum tun kafin a kammala bincike ba.

Source: Facebook
Atiku ya ragargaji gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗaya daga cikin gwamnatocin da suka fi jefa Najeriya cikin wahala.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da sanya rayuwar yau da kullum ta yi tsada matuƙa, yayin da gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi da abin da ya kira “tsananin sha’awar karɓar bashi”.
Asali: Legit.ng

