Yadda Mahaukacin Kare ya Illata Mutane 18 a Jihar Kano

Yadda Mahaukacin Kare ya Illata Mutane 18 a Jihar Kano

  • Akalla mutane 18 ne aka ruwaito cewa wani kare ya cije su a Garko da wasu garuruwan makwabta a jihar Kano a Najeriya
  • NFSS ta fara neman karen da wasu karnuka biyu da ake zargin sun kamu da cutar hauka mai illata jikin mutane bayan cizo
  • Hukumar ta bukaci mazauna yankin su kai rahoton karnukan da ke nuna alamun cutar kuma su garzaya asibiti idan kare ya cije su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano — Akalla mutane 18 ne aka ruwaito cewa wani kare da ake zargin yana dauke da cutar hauka ya cije su a karamar hukumar Garko ta jihar Kano.

Bayan faruwar lamarin, Hukumar Tsaron Daji ta Najeriya (NFSS), reshen Garko, ta fara neman karen da wasu karnuka biyu da ake zargin sun kamu da cutar.

Wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar NFSS ta jihar Kano, CSF Usman Abdullahi Umar, ya sanya wa hannu, an ce ofishin hukumar na Garko ne ta bayyana rahoton faruwar lamarin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk da sulhun da gwamna ya yi, Fulani sun bi dare sun yi wa mutane kisan rashin imani

Mahaukacin kare ya ciji mutane a Kano
Jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya
Source: Original

Mutane 18 sun ji rauni

Sanarwar ta ce karen ya fara kai hari tare da cizon mutane 11 a garin Garko, kafin daga bisani ya tsallaka zuwa wasu kauyukan da ke makwabtaka da garin.

An ce wasu mutane bakwai sun sake fuskantar harin a garuruwan Raba, Kadage, Gurjiya da Dausai, lamarin da ya sa adadin wadanda aka ruwaito kare ya ciza ya kai 18.

Ana neman karnukan

NFSS ta ce ana kuma zargin wasu karnuka biyu da kamuwa da cutar hauka, abin da ya kara tayar da fargabar yiwuwar cutar ta bazu tsakanin dabbobi da mazauna yankin.

Bayan samun rahoton, jami'an NFSS karkashin jagorancin Jami'in Kula da Dajin na Garko, Auwalu Muhammad, sun shiga yankunan da lamarin ya shafa domin neman karnukan da ake zargin sun kamu da cutar.

Hukumar ta ce an kaddamar da aikin ne domin hana sake kai hare-hare da kuma dakile yiwuwar yaduwar cutar haukar kare a yankunan da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

An gargadi mazauna

NFSS ta bukaci mazauna Garko da sauran garuruwan da ke makwabtaka da yankin su kasance cikin taka-tsantsan.

Ta kuma bukaci su rika kai rahoton karnukan da ke yawo ba tare da mai kula da su ba ko dabbobin da ke nuna alamun cutar hauka zuwa ofishin NFSS mafi kusa ko wasu hukumomin tsaro.

Hukumar ta kuma shawarci duk wanda kare ya cije shi ko ya yi mu'amala da dabbar da ake zargin tana dauke da cutar hauka da ya garzaya asibiti domin samun kulawar likita.

NFSS ta ce jami'anta za su ci gaba da bincike a yankunan da lamarin ya shafa har sai an shawo kan barazanar.

Yadda mahaukaci ya yi gudun na tsira

A wani labarin kuma, mahaukaci ya tsallake rijiya da baya a shataletalen Kpakungu a Minna babban birnin jihar Niger a ranar Laraba 17 ga watan Mayu.

Mahaukacin wanda ke kwance a bakin hanya ya sha da kyar ne bayan wani direban babbar mota kirar Mitsubishi dauke da kayan gwari ya nufo kansa a kokarin kaucewa kamun jami’in dan sanda.

Jami’in dan sandan ya biyo direban ne tun daga kauyen Paiko akan hanyar Minna zuwa Abuja saboda yaki ba da kudin goro da aka tsaida shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng