
Jihar Osun







Gwamnatin jihar Osun ta bayyana takaicin yadda wasu 'yan APC ke da ra'ayin neman a bayyana dokar ta baci a jihar, kamar yadda Bola Tinubu ya yi a Ribas.

Majalisar dokokin jihar Osun ta fara yunkurin kawo gyaran da zai dokantar da auren musulmi da ƴan addinin gargajiya, kudurin dokar ya kai karatu na 2.

Jam'iyyar APC ta gargadi gwamnan jihar Osun bayan Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan Rivers, Fubara. APC ta ce ko gwamnan Osun ya bi doka ko a dakatar da shi.

Bayan shafe shekaru ana rigima kan limancin masallaci, Kotu da ke Osun a yankin Iragbiji ta ci gaba da sauraron karar da ke tsakanin wadanda ke takarar kujerar.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi wani jigoɓda ya dawo APC a jihar Oyo. Ya bayyana cewa jam'iyyar za ta kwato Osun, Oyo a hannun PDP.

Jami’ar OAU ta shiga alhini bayan Farfesa Jimoh Olanipekun ya yanke jiki ya fadi ana taro. An gaggauta kai shi asibiti, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Gwamna Adeleke ya gana da Bisi Akande kan rikicin kananan hukumomi, yana mai cewa gwamnatinsa na bin doka. Akande ya bukaci zaman lafiya da bin doka a Osun.

Bayan gargadin gwamnatin Bola Tinubu kan sake zaben kananan hukumomi, Gwamna Ademola Adeleke ya dage cewa za a gudanar da zaben a Osun a gobe Asabar.

Tinubu ya amince da sabbin jami’o’i a Ekiti da Osun don inganta noma, fasaha da muhalli, tare da bunkasa tattalin arziki da kirkire-kirkire a Najeriya.
Jihar Osun
Samu kari