Ba Wasa: Iran Ta Yi Gargadi Mai Zafi ga Masu Shirin Kai Mata Hari
- Iran ta ce duk wani hari da aka kai mata zai fuskanci martani mai ƙarfi ta amfani da sababbin fasahohin soja da na’urorin kariya da ƙasar ke ƙerawa
- Kakakin rundunar sojin Iran ya ce makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na ƙasar sun ƙara ƙarfi da inganci fiye da baya
- Iran ta ce ta sauya dabarun yaƙinta daga tsarin yaƙi na gargajiya zuwa yaƙin da ba ya bin tsarin gargajiya, tare da dogaro da fasahar cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Tehran, Iran - Kakakin rundunar sojin Iran, Birgediya Janar Abolfazl Shekarchi, ya yi gargadi kan kai wa kasar hari.
Kakakin rundunar sojojin ya yi gargadin cewa duk wani hari da aka kai wa ƙasar zai fuskanci martani ta amfani da “sabbin fasahohin soja”.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta ce Shekarchi ya bayyana hakan ne a wata hira da kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran,

Kara karanta wannan
Babbar magana: Amurka da Isra'ila na yunkurin haɗa wasu ƙasashen musulmi faɗa da juna
Shekarchi ya ce rundunar sojin ƙasar ta ƙara ƙarfi sakamakon sauya dabarunta zuwa yaƙin da ba ya bin tsarin gargajiya da kuma ƙara dogaro da fasahar tsaro da ake ƙerawa a cikin gida.
Ya ce Iran a yanzu ta fi kasancewa cikin shiri idan aka kwatanta da lokutan baya da ta fuskanci tashe-tashen hankula da Amurka da Isra’ila.
Iran ta ce makamai da jiragen yaƙi sun ƙara ƙarfi
Shekarchi ya ce rundunar sojin Iran tana cikin “kyakkyawan yanayi”, yayin da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na ƙasar suka samu ƙarin ci gaba.
“Rundunar sojin Iran tana cikin kyakkyawan yanayi. Makaman Iran masu linzami da jirage marasa matuƙa sun ƙara ci gaba da ƙarfi, kuma a wannan karon muna da wasu abubuwan mamaki da muka tanadar wa abokan gaba.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa Iran za ta mayar da martani ga duk wani hari da abokan gabanta za su iya kai mata ta amfani da sabbin fasahohin soja.
Iran na amfani da dabarun yaƙi marasa tsada
A cewar Shekarchi, dabarar yaƙin da Iran ke bi ta mayar da hankali ne wajen tunkarar makamai masu tsada da nauyi ta hanyar amfani da na’urorin kariya masu ƙarancin kuɗi, amma masu inganci da amfani.
Ya ce wannan tsarin ya bai wa Iran damar fuskantar ƙasashen da ke da manyan kayan yaƙi ba tare da dogaro da irin waɗannan makamai masu tsada ba.
Yadda Iran ta fara bunƙasa ƙarfin sojinta
Shekarchi ya ce ƙoƙarin Iran na ƙarfafa ƙarfin sojinta ya samo asali ne tun lokacin yaƙin Iran da Iraq a shekarun 1980
Ya ce a lokacin, rundunar sojin Iran ta fara neman hanyoyin inganta ƙwarewar yaƙi da kuma amfani da sababbin fasahohin zamani.
“A lokacin Yaƙin Tilastawa na farko, yayin da take kare Iran, rundunar sojin ƙasar ta yi ƙoƙarin ƙara ƙarfin yaƙinta da amfani da sabbin fasahohin zamani.” In ji shi.
Ya ce fara shirin bunƙasa makamai masu linzami na Iran a lokacin yaƙin na daga cikin manyan misalan wannan yunƙuri.

Source: Getty Images
Iran ta zargi Amurka da Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce Isra’ila da Amurka suna ƙoƙarin haɗa ƙasashen Musulmi faɗa da juna domin su samu damar sarrafa arzikin yankin.
Shugaba Pezeshkian ya yi zargin ne yayin ake ci gaba da musayar wuta da nuna wa juna yatsa tsakanin kasar Iran da Amurka da Isra'ila.
Asali: Legit.ng

