Ana Wata ga Wata: Sarki Aminu Ya Fito, Gwamnatin Kano ta Bayar da Umarni kan Hawa

Ana Wata ga Wata: Sarki Aminu Ya Fito, Gwamnatin Kano ta Bayar da Umarni kan Hawa

  • Gwamnatin Kano ta dakatar da dukkan jerin gwanon hawa da ayyukan hawan dawaki a cikin birnin Kano saboda dalilan tsaro
  • Majalisar Tsaro ta Jihar ta ce yawan tattara magoya baya da ke da alaƙa da shirye-shiryen na iya haifar da arangama da karya doka
  • Dakatarwar ta fara aiki nan take kuma za ta ci gaba da kasancewa har sai gwamnati ta ba da wata sanarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan jerin gwanon hawa da ayyukan hawan dawaki a cikin birnin Kano.

Gwamnatin ta bayyana cewa matakin ya zama dole saboda dalilan tsaro da kuma hana yiwuwar barkewar rikici.

An hana hawa a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mai magana da yawun bakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya alfarma a 2027, ya fadi dalilin neman tazarce

Gwamnatin ta sanar da matakin ne ranar Lahadi, 27 ga watan Satumban 2026 bayan kammala wani taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Kano.

Majalisar tsaro ta yi nazari kan halin da ake ciki

A yayin taron, jami’an tsaro da sauran mambobin majalisar sun duba yanayin tsaro da ya shafi shirye-shiryen gudanar da ayyukan hawa da hawan dawaki.

A cikin sanarwar da Sanusi ya fitar, gwamnati ta ce majalisar ta yanke shawarar dakatar da ayyukan a matsayin matakin kariya.

Ta ce manufar ita ce kare zaman lafiya da kuma hana yiwuwar asarar rayuka da lalata dukiyoyi.

An ji tsoron yiwuwar arangama

Gwamnatin ta ce bayanan da jami’an tsaro suka tattara sun nuna cewa ana samun gagarumin tattara magoya baya dangane da shirye-shiryen ayyukan.

A cewar gwamnatin, hakan ya haifar da fargabar yiwuwar samun arangama tsakanin ɓangarori daban-daban da kuma lalacewar doka da oda.

Kara karanta wannan

Magu: Bukola Saraki ya samu abin magana da kotu ta wanke shi a sabaninsa da Buhari

An umarci jami’an tsaro su tabbatar da bin umarnin

Gwamnatin ta umarci dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa a jihar da su tabbatar da aiwatar da dokar dakatarwar.

Ta kuma ce a ɗauki matakin da doka ta tanada kan duk wanda aka samu yana karya umarnin.

Haka kuma, gwamnatin ta yi gargaɗi kan duk wani abu ko ɗabi'a da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaron jama'a a jihar.

Gwamnati ta yi kira da a kwantar da hankali

Gwamnatin Kano ta yi kira ga mazauna jihar, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankali.

Gwamnatin ta tabbatar wa mazauna jihar cewa tana ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a faɗin jihar.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma za ta ci gaba da kasancewa har sai an ba da wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amnesty ta yi zarge zarge masu nauyi kan gwamnatin Abb

Sarki Aminu ya fito hawa

Legit Hausa ta fahimci cewa umarnin na zuwa ne bayan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi shirin gudanar da hawan Fatahu a Kano.

Wasu hotuna da Kabiru Umar Inuwa ya dora a shafinsa na Facebook, sun nuna Sarki Aminu ya fito daga fadarsa zuwa gidansa na Mandawari a cikin gari.

Sarki Aminu ya yi shiri na hawa a fitowarsa inda dumbin mutane suka rika daga masa hannu yayin da yake wucewa.

Gwamnatin Kano ta dakatar da hawa
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarki Aminu Ado Bayero da jama'arsa Hoto: Isah Muhammed Salisu, Kabiru Umar Inuwa
Source: Facebook

Sanusi II ya bayar da shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a kara ware harkokin addini da siyasa a Najeriya.

Sanusi II ya ce ya kamata shugabannin addini su mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi addini, yayin da ‘yan siyasa za su mayar da hankali kan tafiyar da gwamnati da inganta rayuwar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng