Hukuncin Kotun Koli Ya Hana Sheikh Pantami Neman Takarar Gwamna a PDP? Bayanai Sun Fito

Hukuncin Kotun Koli Ya Hana Sheikh Pantami Neman Takarar Gwamna a PDP? Bayanai Sun Fito

  • Magoya bayan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami sun ce hukuncin Kotun Koli ba zai hana dan takararsu neman kujerar gwamnan Gombe a 2027 ba
  • Kotun Tarayya ta soke zaben fidda gwani na PDP da ya tsayar da Pantami, tare da umartar jam’iyyar ta gudanar da sabon zaben fidda gwani
  • PDP ta sanya Talata, 29 ga Satumba, 2026 domin gudanar da sabon zaben fidda gwani, inda ta tantance Pantami da wasu ‘yan takara biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Magoya bayan tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, sun dage cewa sabon hukuncin Kotun Koli bai shafi dan takararsu ba.

A cewarsu, hukuncin kotun bai haramta wa Pantami neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe karkashin inuwar jam'iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya musanta cewa hukuncin Kotun Koli ya taba takarar Pantami

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa hakan ya biyo bayan wasu hukuncin aka yanke ranar Alhamis, inda Kotun Koli ta maido da wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026 da suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu da tsayar da ‘yan takara.

A bangare guda, Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaben fidda gwani na PDP da ya samar da Pantami a matsayin dan takarar gwamna, tare da umartar jam’iyyar ta sake gudanar da zaben fidda gwani.

Pantamiyya ta yi martani

Kungiyar Pantamiyya Movement, a cikin wata sanarwa da kakakinta, Ibrahim M. Alfathir, ya sanya wa hannu, ta ce ta amince da hukuncin Kotun Tarayya.

Ta bayyana cewa hukuncin bai hana Pantami shiga wani sabon zaben fidda gwani na PDP ba, tana mai cewa ikirarin cewa an cire Pantami daga takarar yaudara ne.

Kungiyar ta ce Pantami zai shiga sabon zaben fidda gwani kamar yadda kotun ta umarta.

Magoya bayan Pantami sun dage

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana so Tinubu ya hakura da shiga takarar zaben 2027

Magoya bayan Pantami, ciki har da Abdullahi Mohammed, Suwaiba Musa da wasu, sun ce babu wani daga cikin hukuncin Kotun Tarayya ko sabon hukuncin Kotun Koli da ya kawo karshen aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Gombe.

Matsayar tasu ita ce Pantami har yanzu yana da damar shiga sabon zaben fidda gwani na PDP.

Yunkurin samun karin bayani daga kakakin Pantami bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami tare da dandazon magoya baya a jihar Gombe Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Kotun Koli ta maido da tanade-tanade

A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis kan dokokin zaben Najeriya, Kotun Koli ta maido da sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na Dokar Zabe ta 2026.

Tanade-tanaden sun fi mayar da hankali ne kan rajistar mambobin jam’iyyu da kuma yadda ake tsayar da ‘yan takara.

A karkashin sashe na 77(5), Kotun Koli ta ce mambobin jam’iyya da sunayensu ke cikin rajistar mambobin da aka mikawa Ikwanaki 21 kafin zaben fidda gwani ne kadai ya halasta su shiga zaben.

PDP ta tantance Pantami a Gombe

Kun ji cewa PDP ta tantance Farfesa Isa Ali Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry domin su fafata a sabon zaɓen fitar da dan takarar gwamna na jihar Gombe.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa za a gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani na jihar Gombe ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262