Amurka Ta Gode Wa Birtaniya da Wasu Kasashen Musulmi 3 kan Goyon bayan Yaki da Iran

Amurka Ta Gode Wa Birtaniya da Wasu Kasashen Musulmi 3 kan Goyon bayan Yaki da Iran

  • Ministan Baitulmalin Amurka Scott Bessent ya gode wa Birtaniya, Turkiyya, Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa kan aiwatar da takunkumin Iran
  • Bessent ya ce wasu kamfanonin jiragen sama na Iran sun dakatar da zirga-zirga zuwa wasu ƙasashe, yayin da wasu bankuna suka dakatar da mu’amalar kuɗi da Tehran
  • Amurka ta yi barazanar kakaba ƙarin takunkumi kan kamfanonin da ke hulɗa da kamfanonin jiragen saman Iran da ke ƙarƙashin takunkumi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Ministan Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya gode wa gwamnatocin Birtaniya, Turkiyya, Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Scott Bessent ya gode wa kasashen ne kan goyon bayan yaƙin tattalin arzikin da Washington ke yi da Iran.

Amurka ta gode wa kasashe
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Scott Bessent ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Asabar, 26 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta nema a taron UNGA karo na 81

Ya ce ya tura tawagar jami’ai zuwa sassa daban-daban na duniya domin matsa lamba kan ƙasashe su ɗauki matakai bayan ƙaddamar da abin da ya kira “Operation Economic Outcast”.

“Waɗannan ƙoƙarin suna haifar da sakamako,” ya rubuta.

An dakatar da wasu zirga-zirgar jiragen Iran

Bessent ya ce Turkiyya da Oman sun sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kamfanin Mahan Air zuwa ƙasashensu.

Ya kuma ce UAE ta dakatar da dukkan jiragen kamfanonin jiragen saman Iran, yayin da wasu manyan bankunan kasuwanci a UAE da Turkiyya suka dakatar da gudanar da mu’amalar kuɗi da Iran.

“Ina godiya ga gwamnatocin Birtaniya, Turkiyya, Oman da UAE. Za mu ci gaba da aiki tare, domin har yanzu akwai ƙarin matakan da ya kamata a ɗauka,” in ji shi.

Bessent ya ce manufar matakan ita ce hana Tehran aiwatar da abin da ya kira “ajandar ta’addanci”.

Amurka ta yi barazanar ƙarin takunkumi

Amurka ta kuma yi barazanar kakaba takunkumi kan kamfanonin da ke gudanar da harkokin kasuwanci da kamfanonin jiragen saman Iran da aka sanya wa takunkumi.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi: An nemi wasu jiga jigan ADC an rasa a kwamitin yakin neman zaben Atiku

Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da wasu jiragen Iran zuwa biranen Iraq guda huɗu, wato Baghdad, Najaf, Erbil da Sulaimaniyah.

Gwamnatin Iraq ta ce tana tattaunawa da Washington domin neman keɓancewa daga takunkumin saboda dalilan jinƙai.

UAE ta dakatar da jiragen kamfanonin Iran

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta UAE ta sanar da dakatar da dukkan zirga-zirgar kamfanonin jiragen saman Iran saboda takunkumin Amurka.

UAE na da ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin zirga-zirgar jiragen sama a Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na Iran, Tasnim, ya kuma ruwaito cewa an dakatar da wasu jiragen zuwa Oman, Georgia da Azerbaijan.

Amurka ta yi godiya ga wasu kasashe
Scott Bessent na ganawa da jami'in gwamnatin China Hoto: @SecScottBessent
Source: Twitter

IRGC ta yi barazana ga Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta Iran ta yi barazanar kai hare-hare idan har aka sake kaddamar da yaki kan kasar.

Rundunar ta yi barazanar kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka hari, ciki har da waɗanda ke cikin Tekun Indiya, idan Washington ta ƙaddamar da wani sabon yaƙi da Tehran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng