INEC na da 'Yan Takara ko Jam'iyyar da Take Goyon Baya a Zaben 2027? An Samu Bayanai
- Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya yi maganar goyon bayan wani dan takara ko jam'iyya a zaben 2027
- Amupitan ya bayyana cewa INEC ta fara shirye-shiryen zaɓen 2027 da wuri domin gwadawa, tantancewa da ƙarfafa tsarin gudanar da zaɓe
- Ya roƙi sarakunan gargajiya su yi amfani da tasirinsu wajen hana tashin hankali da amfani da matasa wajen rikicin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya yi magana kan zaben 2027.
Farfesa Amupitan ya sake tabbatar da cewa hukumar ba ta da ɗan takara ko wata jam’iyyar siyasa da take goyon baya a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Amupitan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ga Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, a wani ɓangare na shirye-shiryen hukumar gabanin babban zaɓen 2027, kamar yadda hukumar ta sanar a shafinta na X ranar Lahadi, 27 ga watan Satumban 2026.
Amupitan ya gana da Sarkin Zazzau
Shugaban INEC ya samu rakiyar Kwamishinonin Ƙasa na hukumar, Shugaban Ma’aikata da sauran mataimaka na musamman.
Daraktocin hukumar ma sun raka tawagar zuwa fadar Sarkin Zazzau na 19, inda Amupitan ya bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar ganawar masu ruwa da tsaki gabanin ayyukan zaɓen 2027.
Ziyarar na daga cikin shirye-shiryen INEC na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki yayin da take ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
INEC ta fara shirin zaɓen 2027 da wuri
Shugaban INEC ya ce hukumar ta fara shirye-shiryen zaɓen tun da wuri saboda girma da kuma rikitarwar gudanar da zaɓe a Najeriya.
Ya ce INEC ta daina dogaro da shirye-shirye a kurarren lokaci, inda yanzu take gwadawa, tantancewa da ƙarfafa tsarin aikinta tun kafin zuwan zaɓen 2027.
Amupitan ya tabbatar wa Sarkin Zazzau cewa INEC ta himmatu wajen tabbatar da tsaka-tsaki, adalci da gaskiya a lokacin gudanar da zaɓe.
“Ba mu da ’yan takara, ba mu da wata jam’iyyar siyasa, ba mu da wata manufa face tabbatar da muradin ’yan Najeriya, waɗanda su ne masu iko,” in ji shi.
Ya roƙi sarakuna su hana tashin hankali
Shugaban INEC ya kuma roƙi Sarkin Zazzau da ya yi amfani da tasirinsa wajen ba jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu shawarar guje wa tashin hankali da yaɗa kalaman ƙiyayya.
A cewarsa, bai kamata a ɗauki zaɓe a matsayin wani abu na “rayuwa ko mutuwa” ba, sai dai a matsayin hanyar da ’yan ƙasa ke bayyana zaɓinsu cikin lumana.
Ya kuma yi kira na musamman ga sarakunan gargajiya da su hana matasa bari a yi amfani da su wajen aikata rikicin siyasa.
Amupitan ya ce zaman lafiya da amincewar jama’a suna da muhimmanci wajen tabbatar da ingantaccen tsarin dimokuraɗiyya yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen 2027.

Source: Facebook
Mukhtar Ahmad ya bayyana cewa INEC ta saba yin irin wadannan alkawuran a baya amma sai daga baya a ga labarin ba haka yake ba.
"Muna fatan Allah ya sa da gaske yake yi, amma dai mun sha jin irin wadannan alkawuran a baya. Daga baya sai a ga kamar ana fifita wasu musamman masu gwamnati a hannunsu." In ji shi.
SERAP ta kai INEC kara kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta kai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kotu.
Kungiyar SERAP tana zargin hukumar da kasa bayyana iyakar kudaden da za a iya bayarwa a matsayin gudunmawar siyasa gabanin babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng


