Bayan Atiku Ya Lashe Zaben TMG, Abba Hikima Ya Koma Bayan ADC

Bayan Atiku Ya Lashe Zaben TMG, Abba Hikima Ya Koma Bayan ADC

  • Abba Hikima ya bayyana cewa ya hakura da marawa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso baya a zaben 2027, inda ya koma tafiyar Atiku Abubakar
  • Lauyan ya ce matakin ba wai saboda ya daina yarda da Obi da Kwankwaso ba ne, sai dai saboda burinsa na ganin an samu hadin kai a zabe mai zuwa
  • Ya kuma yi kira ga masu zabe da su hada kai wajen marawa Atiku Abubakar baya domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Abba Hikima ya bayyana cewa ya koma goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar bayan sakamakon zaben gwaji na TInubu Must Go.

Ya yi magana yana mai cewa ya hakura da marawa Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso baya a wannan kakar zabe.

Kara karanta wannan

Majiyoyi sun tsaida lokacin da ake sa ran Tinubu zai dawo Najeriya daga Turai

Atiku Abubakar da Abba Hikima
Atiku Abubakar a hagu da Abba Hikima a dama. Hoto: Atiku Abubakar Abba Hikima
Source: Facebook

Abba Hikima ya bayyana matsayarsa ne a wani sako da ya wallafa a Facebook, inda ya ce burinsa shi ne ganin an samu hadin kan da zai kawo sauyin gwamnati a Najeriya.

Abba Hikima ya koma tafiyar Atiku

Hikima ya ce sakamakon zaben gwajin ya sa ya yanke shawarar daina marawa Obi da Kwankwaso baya a wannan kakar zabe.

Ya ce:

“Na hakura da marawa Peter Obi da Sanata Kwankwaso baya a wannan kakar zabe. Ba don bana son su ba, a’a, sai saboda na fi son Najeriya, al’ummata da kuma duk wani hadin kan da zai kai mu ga canja gwamnatin Tinubu.”

Ya yi fatan Allah ya bai wa Atiku nasarar kayar da Tinubu da gagarumar tazara, tare da addu’ar cewa idan ya yi nasara, Allah ya sanya hakan ya zama sanadin samun sauki da tsaron al’umma.

Atiku Abubakar da mataimakinsa
Atiku Abubakar da abokin takarar shi, Rotimi Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Dalilin neman hada kai

Abba Hikima ya ce a baya ya kasance yana kira ga ‘yan takara da su hada kai, ko kuma masu zabe su taru su mara wa dan takara guda baya domin kawo sauyi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya alfarma a 2027, ya fadi dalilin neman tazarce

Ya bayyana cewa kiran nasa na hadin kai ba yana nufin bai yarda da Obi da Kwankwaso ba ne, inda ya ce yana da yakinin cewa dukkaninsu sun fi Tinubu nagarta.

Abba Hikima ya ce:

“Kada rashin hadewar ‘yan takara ya ba mu tsoro. Hadin kan masu zabe dai-dai yake da hadin kan shugabanni ko jam’iyyu. Idan muka ajiye bukatunmu na kashin kai muka hade a bayan daya mai karfi, tsaf za mu kada shi cikin sauki.”

Batun kayar daTinubu a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi ikirarin cewa mutanen da suka yi adawa da Goodluck Jonathan a zaben 2015 ne ke hada kai domin kalubalantar Bola Tinubu a zaben 2027.

Okpebholo ya bayyana hakan ne yayin bikin fara aikin gyaran hanyar Benin-Asaba, inda ya ce babu gurbi a fadar shugaban kasa kuma bai kamata a sauya shugaban da ke aiki ba.

Ya ce wasu daga cikin masu son kalubalantar Tinubu sun taba rike mukamai daban-daban, yana mai zargin cewa sun yi adawa da Jonathan a 2015 lokacin da yake kokarin kafa makarantun Almajirai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng