2027: 'Yan Daba Sun Mamaye Jami'an INEC, Sun Sace Katunan Zabe

2027: 'Yan Daba Sun Mamaye Jami'an INEC, Sun Sace Katunan Zabe

  • Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari cibiyar rabon katin zaɓe ta INEC da ke jihar Osun tare da kwashe wasu katunan zaɓe na dindindin (PVC)
  • Maharan sun harba bindiga sama domin tarwatsa jama'a kafin su tsere da katunan PVC, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici
  • Rundunar 'yan sandan Osun ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an fara bincike domin kamo waɗanda suka kai harin tare da ƙwato katunan da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Osogbo – Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari wata cibiyar rabon katin zaɓe ta Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke makarantar Oyinlola DC School a garin Okuku na jihar Osun.

Maharan sun tarwatsa aikin rabon katin zaɓen na dindindin (PVC) tare da tserewa da wasu fakitocin katunan zaɓe, lamarin da ya jefa mutanen da ke wurin cikin firgici.

Kara karanta wannan

Matar aure ta kwarawa kishiyarta mai ciki ruwan zafi, ta haihu dan ya mutu

Katin zabe na Najeriya
Wasu katunan PVC na hukumar INEC. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da jami'an INEC ke rabon katunan PVC ga masu karɓa a cibiyar.

Yadda 'yan daba suka kai harin

Wani mazaunin garin Okuku mai suna Gbadebo ya bayyana cewa maharan sun shiga harabar makarantar ba tare da mutane sun ankara ba kafin daga bisani su fara harbe-harbe sama.

Ya ce mutanen da ke wurin sun rika gudu domin tsira da rayukansu, yayin da maharan suka nufi inda jami'an INEC suka ajiye PVC suka kwashe su.

A cewarsa:

"Lamarin ya faru ne a makarantar Oyinlola DC School da ke Ward 2 a Okuku. Muna jiran karɓar PVC lokacin da 'yan daban suka shigo."

Channels TV ta wallafa cewa ya ƙara da cewa:

"Sun harba bindiga sama, kowa ya rika gudu. Daga nan suka tafi kai tsaye inda aka ajiye katunan PVC suka ɗauki katunan. Kimanin mutum takwas ne suka zo."

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Yan Najeriya na fuskantar sabuwar barazana ta tsadar abinci

'Yan sanda sun fara bincike

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Ibrahim Gotan, ya yi Allah wadai da harin tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.

Ojelabi ya ce an tura jami'an tsaro da na leƙen asiri domin kamo maharan da kuma ƙwato wasu katunan PVC da aka sace.

Shugaban hukumar INEC
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da duk wanda ke da sahihan bayanai game da harin da ya kai rahoto ofishin 'yan sanda mafi kusa ko kuma ya tuntubi rundunar.

INEC ta yi rajistar masu zaɓe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi rajistar sababbin masu zaɓe 6,885,330 a matakai uku na aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR).

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Hukumar ta ce za ta nuna kundin rajistar masu zaɓe a watan Agusta domin karɓar ƙorafe-ƙorafe da gyare-gyare kafin kammala aikin tantance bayanan masu rajista.

Sai dai wani jami'in INEC ya bayyana cewa adadin ya gaza hasashen da hukumar ta yi na samun sababbin masu zaɓe miliyan 10 kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng