Majalisa Za Ta Dauki Mataki Ganin Tinubu Ya Kara Hutu ba tare da Ba Kashim Mulki ba
- 'Yan majalisar Najeriya da ke inuwar SDG sun bukaci Majalisar Tarayya ta dawo zama na musamman
- Ana so a ayyana Mataimakin Shugaban Kasa a matsayin Mukaddashin Shugaba tunda Bola Tinubu bai nan
- An ce kundin tsarin mulki ya ba majalisa damar nada Shugaban rikon kwarya kamar yadda aka gani a 2010
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wasu ‘yan majalisar wakilan Najeriya a karkashin Save Democracy Group (SDG) sun bukaci a bude zaure a zauna.
‘Yan majalisar tarayyan suna so a yi zama na musamman duba duba lamarin hutun da Bola Ahmed Tinubu yake yi a kasar waje.

Source: Getty Images
Kila a bude majalisa saboda hutun Bola Tinubu
Jaridar Premium Times ta ce abin da ya kawo wannan kuwa shi ne ganin cewa Shugaban kasa ya tafi ba tare da ya mika mulki ba.
Duk da Tinubu ya tsawaita hutun da yake yi a waje, bai rubuta takarda cewa Kashim Shettima ya zama shugaban rikon kwarya ba.
Kungiyar ta fitar da jawabi a makon nan ta hannun Awaji-Inombek Abiante (NDC, Rivers) da Abubakar Kusada (APC, Katsina).
‘Yan majalisar tarayyar sun duba sashe na 21 na tsarin mulki wanda ya ce shugaban kasa zai iya tafiya hutu ne na kwanaki 21 kawai.
Yanzu kwanakin sun kare kuma Tinubu bai dawo ba sannan bai mika iko ba. Bayan haka an ki bayyana kwanakin da zai kara a waje.
Ana so Kashim Shettima ya karbi mulki
Duk da ya yi umarni Shettima ya wakilci Najeriya a Majalisar dinkin duniya, shugaban kasar bai yarda ya mika ragama gare shi ba.
A wasu lokutan kuma, rahoton ya ce George Akume yake wakiltar Tinubu. Wannan ya jawo SDG ta ke ganin ya kamata su yi zama.
Kungiyar SDG tana ganin ko da shugaban kasa bai aika wa shugabannin majalisa takardar mika mulki ba, su suna da hurumin yin hakan.
Idan aka yi aiki da sashe na 145(2), ‘yan kungiyar suna ganin majalisa za ta iya sa Shettima ya zama shugaban kasa na rikon kwarya.
Jawabin ya bayyana cewa da Duma Boko ya yi tafiya, haka aka bi har mataimakinsa ya zama shugaban riko a kasar Botswana.
Majalisa ta taba yin haka lokacin Yar'adua
‘Yan majalisar sun fada wa Godswill Akpabio da Abbas Tajudeen su kira zama a tattauna kamar yadda The Guardian ta ruwaito.
‘Yan SDG suna da magabata domin kuwa an yi amfani da kundin tsarin mulki lokacin da Umaru Yar’Adua ya yi irin haka a 2009.
Marigayi shugaba Yar’Adua ya tafi asibiti a Saudi aka dade ba tare da ya mika mulki ga mataimakinsa Goodluck Jonathan ba.
Bayan kwanaki kusan 80, ‘yan majalisa suka rantsar da Jonathan a babin lalura saboda gudun a bar Najeriya babu wani shugaba.

Source: Getty Images
'Yan Najeriya sun saye kadarorin $270m a Amurka

Kara karanta wannan
"Zan iya rantsewa," Tsohon gwamna ya ce bai taba ganin shugaba kai tsari kamar Tinubu ba
Wani sabon rahoto ya tona wa jami’an gwamnati da ‘yan siyasar Najeriya asiri kamar yadda wani dogon rahoto ya zo kwanan nan.
An fahimci 'yan Najeriya da dama sun saye kadarori na biliyoyin kudi a Amurka a cikin shekaru 35 daga karshen mulkin sojoji zuwa yau.
Mutane 61 sun tara dukiya ta hanyar amfani da kudin da ba a san tushensu ba, suka mallaki manyan gidaje na $270m a kasr Amurka.
Asali: Legit.ng

