An Cafke Wata Mata da Ta Yi Yunkurin Shigar da Barasa Gidan Yarin Najeriya
- NCoS ta cafke Balikis Shobowale bisa zargin yunkurin shigar da barasa gidan gyaran hali na Ibara da ke jihar Ogun a Kudu maso Yammacin Najeriya
- An gano mahadin barasa ethanol da ta boye a cikin sinkin ruwan gora tare da nuna shi tamkar ruwan sha ne ga jami'an tsaro
- Hukumar ta ce duk wanda ya yi yunkurin safarar haramtattun kayayyaki zai fuskanci hukuncin doka kamar yadda aka shar'anta a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Ogun — Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS), reshen jihar Ogun, ta cafke wata mata mai suna Balikis Shobowale bisa zargin yunkurin shigar da barasa zuwa gidan gyaran hali na Ibara da ke Abeokuta.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar a Ogun, Olayinka Odukoya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abeokuta ranar Lahadi.
An cafke ta wajen bincike
Odukoya ya ce an cafke matar ne da misalin karfe 3:50 na yammacin Asabar yayin aikin binciken tsaro na yau da kullum a cibiyar.

Source: Original
Ya ce jami'an tsaro sun gano sinadarin ethanol da aka boye a cikin sinkin ruwan gora tare da nuna shi tamkar ruwan sha da aka tanadar wa wani fursuna.
Ya ce nan take aka tsare wadda ake zargin kafin daga bisani a mika ta ga 'yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.
Hukumar ta yi gargadi
Jami'in kula da gidajen gyaran hali na jihar Ogun, Abioye Adesina, ya yaba wa jami'an da suka gano lamarin saboda taka-tsantsan da kuma bin ka'idojin tsaro.
Adesina ya ce hukumar ba ta lamuntar shigar da haramtattun kayayyaki da sauran ayyukan da ka iya kawo cikas ga tsaro a gidajen gyaran hali.
Ya ce kama barasar na nuna kudurin hukumar na kare fursunoni, tabbatar da zaman lafiya da kuma bin doka, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Ya gargadi masu yunkurin shigar da haramtattun kayayyaki cikin gidajen gyaran hali cewa za su fuskanci hukuncin doka cikin gaggawa.

Kara karanta wannan
Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira
Hukumar ta tabbatar wa jama'a cewa za ta ci gaba da daukar matakan hana shigar da haramtattun kayayyaki cikin gidajen gyaran hali tare da kare martabar tsarin gyaran hali.
Gidajen gyaran hali a Najeriya
Gidajen gyaran a kasar sun kasance masu cikakken tsaro da tare da bincike kan wadanda ke kawo ziyara ga 'yan uwansu duk lokacin da suka zo ziyara.
Sai dai, akan samu lokuta da dama da ake shiga da abubuwan da suka saba doka tare da kokarin lalata tsaron cikin gidajen halin Najeriya.
A bangare guda, an sha samun lokuta da dama da aka kai farmakin ta'addanci domin fasa gidan gyaran hali a Najeriya, lamarin da ke daukar hankalin 'yan kasa.
'Yan bindiga sun tsere daga gidan gyaran hali
A wani labarin kuma, tarihin fashin magarkama a Najeriya ya ci gaba a ranar Litinin bayan da fursunoni 16 suka tsere daga gidan yarin Keffi, jihar Nasarawa.
Legit Hausa ta ruwaito cewa fursunonin sun jikkata gandirebobi biyar a lokacin tserewarsu, amma hukumar NCoS ta ce an kamo bakwai daga cikinsu.
A shekarar 2024, Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar wakilai ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin binciken shari’a kan hare-haren gidajen yari a Najeriya.
Asali: Legit.ng
