ADC: 'Abu 1 da zai Hana Jam'iyyar Su Atiku Nasara a Zaɓen Osun'

ADC: 'Abu 1 da zai Hana Jam'iyyar Su Atiku Nasara a Zaɓen Osun'

  • Sakataren yaɗa labaran ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar na da kwarin gwiwar lashe zaben gwamnan Osun da za a gudanar a ƙarshen mako
  • Bolaji Abdullahi ya nuna damuwa kan yawan jami’an soji da sauran jami’an tsaro da aka jibge a Osun, yana cewa hakan na iya jefa shakku kan sahihancin zaben
  • Ya ce ADC ta yi imanin za ta iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, ko da kuwa ba a samu haɗin kan dukkan jam’iyyun adawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – Sakataren yaɗa labaran ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan Osun, Najeem Salaam, zai yi nasara.

Bolaji Abdullahi ya ce abin da ya gani yayin wata ziyara da ya kai Osogbo kwanaki uku da suka gabata ya ƙara masa kwarin gwiwar cewa ADC na da gagarumar damar lashe zaben.

Kara karanta wannan

ADC ta yi zargin ana shirin kama wani babba a jam’iyyar bayan El Rufai

Bolaji Abdullahi ya ce za su yi nasara a zaben Osun
Sakataren yada labaran ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: Mallam Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa za a samu matsalar rashin nasara ne idan ba a yi zaben a cikin gaskiya da nasara kamar yadda ake fargaba.

ADC ta yi magana kan zaben Osun

Jaridar Punch ta ruwaio cewa a lokacin da ya ziyarci Osogboo, ya samu kwarin gwiwa da ya tabbatar masa cewa ADC ce a kan gaba a jihar Osun.

A kalamansa:

“Na kasance cikin tawagar da ta ziyarci Osogbo kwanaki uku da suka gabata. Kafin mu je Osogbo, ina da damuwa kan ko da gaske muna da damar fafatawa wajen neman mulki a Osun a zaben wannan makon. Amma abin da na gani a Osogbo ya ƙara mini kwarin gwiwa cewa idan za a gudanar da zaben cikin ’yanci da adalci, ADC za ta lashe zaben."

Sai dai ya nuna damuwa kan abin da ya kira mayar da siyasar jihar Osun tamkar filin soja, yana cewa yawan jami’an soji da sauran jami’an tsaro da aka tura jihar na iya jefa shakku kan sahihancin zaben.

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun jajubo rigima da jam'iyyar, an ba su wa'adi su gyara alaka da ita

Abin da jama'ar Osun ke dubawa

Bolaji Abdullahi ya ce masu kada kuri’a za su fi duba shirin ɗan takarar na magance matsalolinsu, musamman batun samar da ayyukan yi da jin dadin ’yan fansho, maimakon yadda yake magana da Turanci.

ADC ta yi gargadi cewa a tabbatar da sahihancin zaben Osun
Shugaban INEC na kasa, Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Ya bayyana cewa:

“Mutanen Osun ba za su zabe shi ba saboda yana iya magana da wani irin Turanci. Za su zabe shi ne saboda yana iya magana kan bukatun da suke da su."

Ya kuma ce ba daidai ba ne a yi amfani da sakamakon zabukan baya wajen tantance karfin ADC a Osun, saboda zabukan da ake gudanarwa ba tare da babban zaben kasa ba suna da nasu musamman.

Atiku ya gargadi INEC kan zaben Osun

A baya, kun samu labarin cewa Atiku Abubakar ya gargadi INEC da hukumomin tsaro kan yawaita jami’an tsaro a zaben gwamnan Osun, yana mai cewa zaben gwaji ne ga Najeriya.

Atiku wanda shi ne 'dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce zabe aikin farar hula ne, ba aikin soja ba, yana mai neman a tabbatar da gaskiya da adalci duba da abubuwan da ke faruwa.

Dan takarar shugaban kasar da ke fatan kifar da Bola Tinubu ya kuma bukaci a fayyace bambance-bambancen da aka ruwaito a takardar shaidar karatun shugaba mai ci da aka gabatar wa INEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng