1959 zuwa 2026: Lokuta 5 da Hausawa da Ibo Suka Haɗu a Siyasance kafin Tafiyar OK a NDC
Mutane da dama sun fara bayyana ra’ayoyi mabambanta kan tattaunawar da ake yi game da sabon kawancen siyasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A kwanakin baya ne fitattun ‘yan siyasar biyu suka koma jam’iyyar NDC, inda aka bayyana Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da aka zabi Kwankwaso a matsayin mataimakinsa gabanin zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Nazarin siyasar Najeriya gabanin 2027
Kafin komawarsu NDC, Obi da Kwankwaso sun fara shiga jam’iyyar ADC a lokacin da ake kallonta a matsayin babbar haɗakar jam’iyyun adawa. Sai dai daga baya suka fice daga cikinta, suna mai danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da kuma takaddamar shari’a da suka dabaibaye jam’iyyar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Tun bayan sanar da sabon kawancen, an fara muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin haɗin gwiwar zai iya kawo babban sauyi a siyasar Najeriya, yayin da wasu ke hasashen cewa bambancin ra’ayi tsakanin jagororin na iya haifar da matsala nan gaba.
Sai dai masana tarihi da masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa irin wannan haɗaka tsakanin ‘yan siyasar Arewa da Kudu maso Gabas ba sabon abu ba ne a tarihin siyasar Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa tun kafin Najeriya ta samu ‘yancin kai, shugabannin siyasa daga Arewa da Gabas sukan haɗa kai domin kafa gwamnati, shiga zabe ko gudanar da mulki tare.
A wasu lokuta irin wadannan kawance sun yi nasara, yayin da wasu kuma suka gaza cimma burin da aka kafa su domin shi.
Manyan kawancen siyasar Arewa da Gabas
Ga wasu fitattun lokuta shida da ‘yan siyasar Arewa da Kudu maso Gabas suka haɗa kai a siyasar Najeriya, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa:
1. Tafawa Balewa da Azikiwe: NPC da NCNC a 1959

Source: Getty Images
Babban kawancen siyasa na farko a tarihin Najeriya shi ne haɗin gwiwar jam’iyyun NPC da NCNC a shekarar 1959.
A lokacin, jam’iyyar NPC ƙarƙashin jagorancin Sir Ahmadu Bello ce ta lashe mafi yawan kujeru a zaben tarayya, amma ba ta da rinjayen da zai ba ta damar kafa gwamnati ita kaɗai.
Hakan ya sa aka shiga tattaunawa da jam’iyyar NCNC ta Nnamdi Azikiwe domin kafa gwamnatin haɗaka a matakin tarayya.
Wannan kawance ne ya share hanyar samun ‘yancin kai na Najeriya a shekarar 1960, inda Abubakar Tafawa Balewa ya zama Firaministan ƙasar, yayin da Azikiwe ya zama shugaban ƙasa na farko.
Masana tarihi sun yi imanin cewa haɗin gwiwar ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnatin tarayya ta farko da kuma haɗa yankunan Najeriya wuri guda.
2. Shagari da Ekwueme: Tikitin NPN a 1979

Source: Getty Images
Bayan kusan shekaru 10 na mulkin soja bayan rugujewar Jamhuriya ta Farko, Najeriya ta koma mulkin farar hula a shekarar 1979.
Jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) ta tsayar da Shehu Shagari daga jihar Sokoto a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Jam’iyyar ta kuma zabi Alex Ekwueme daga yankin Arewa maso Gabas a matsayin mataimakinsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kawancen Shagari da Ekwueme ya samu karɓuwa sosai a lokacin saboda ya taimaka wajen rage rabuwar kai tsakanin Arewa da yankin Ibo bayan yakin basasa.
Tikitin ya lashe zaben 1979 kuma ya ci gaba da mulki har zuwa juyin mulkin soja na shekarar 1983.
3. Buhari da Okadigbo: ANPP a 2003

Source: Twitter
A shekarar 2003 ne Muhammadu Buhari ya fara neman kujerar shugaban ƙasa bayan dawowar Najeriya mulkin dimokuradiyya.
Ya tsaya takara ne ƙarƙashin jam’iyyar ANPP domin kalubalantar shugaban ƙasa na lokacin, Olusegun Obasanjo, wanda ke neman wa’adi na biyu.
Domin ƙarfafa tikitin, Buhari ya zabi Chuba Okadigbo daga jihar Anambra a matsayin mataimakinsa, kamar yadda ThisDay Live ta ruwaito.
Ko da yake ba su yi nasara ba, sun samu kuri’u masu yawa, kuma haɗin gwiwar nasu ya zama daya daga cikin fitattun kawancen siyasar Arewa da Gabas a Najeriya.
4. Buhari da Ume-Ezeoke: ANPP a 2007
A zaben 2007, Muhammadu Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ANPP, don sake neman shugabancin kasar bayan rasa damarsa a 2003.
A wancan lokacin, Edwin Ume-Ezeoke ne shugaban jam'iyyar na kasa. Domin gina kawance mai karfi tsakanin Arewa da Kudu, Buhari ya zabi Ume-Ezeoke a matsayin abokin takararsa.
Sai dai, tikitin Buhari da Ume-Zeoke ya sha kasa a babban zaben na watan Afrilun 2007, inda Alhaji Umaru Musa Yar'Adua na jam'iyyar PDP ya samu nasara.
5. Atiku da Peter Obi: Tikitin PDP a 2019

Source: Facebook
A zaben shekarar 2019, jam’iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar da Peter Obi domin kalubalantar gwamnatin APC.
Atiku ya tsaya takarar shugaban ƙasa yayin da Obi ya zama mataimakinsa. An tsara kawancen ne domin haɗa ƙarfin Atiku a Arewa da tasirin Obi a Kudu maso Gabas.
Tikitin ya samu goyon baya sosai musamman a Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas, amma daga ƙarshe bai lashe zaben ba.
Duk da haka, haɗin gwiwar Atiku da Obi har yanzu ana kallonsa a matsayin daya daga cikin fitattun tikitin siyasa a tarihin Najeriya na baya-bayan nan.
6. Obi da Kwankwaso: NDC na harin takarar 2027

Source: Twitter
Sabon kuma mafi yawan ce-ce-ku-ce a kai shi ne kawancen Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso gabanin zaben shekarar 2027.
A zaben 2023, Obi ya tsaya takara ne ƙarƙashin jam’iyyar LP, yayin da Kwankwaso ya tsaya a ƙarƙashin NNPP, amma dukkansu sun gaza kayar da APC.
Yanzu kuma, gabanin 2027, Obi da Kwankwaso sun haɗa kai a ƙarƙashin jam’iyyar NDC domin kalubalantar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
Rahotanni sun ce an cimma yarjejeniya cewa idan NDC ta yi nasara, Peter Obi zai yi wa’adi guda ɗaya kacal kafin daga baya a bai wa Kwankwaso damar tsayawa takara.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Masu goyon bayan kawancen na ganin hakan zai ƙarfafa tsarin rabon mulki tsakanin yankunan Najeriya, yayin da masu suka ke cewa sabanin ra’ayi na siyasa na iya bayyana tun kafin zaben.
Obasanjo ya gana da jagororin Obi/Kwankwaso
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya gana da shugabannin tafiyar Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso (OK Movement).
Cif Olusegun Obasanjo da yan siyasar sun tattauna kan hadin kan kasa da kuma bunkasa siyasar da ta fi mayar da hankali ga talakawa.
Jigon jam'iyyar NDC, Ladipo Johnson, ya ce ganawar za ta kara karfafa manufofin kungiyar yayin da suke tunkarar babban zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



