Sheikh Jingir Ya Sake Fadar Abin da Masu Sukarsa kan Muslim Muslim ba Za Su So ba
- Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ba ya nadamar goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi, duk da sukar da ake yi masa
- Shugaban Majalisar Malaman Izala ya ce matsayinsa ya samo asali ne daga abin da ya kira nauyin da ke kansa a matsayinsa na Musulmi
- Jingir ya ce zai ci gaba da ƙarfafa Musulmai su goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi, duk da sukar da ake yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jos - Malamin addinin Musulunci kuma shugaban Majalisar Malaman Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce ba ya nadamar goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi.
Sheikh Jingir ya bayyana cea baya nadamar ne duk kuwa da irin sukar da kalamansa na baya-bayan nan suka jawo.

Source: Facebook
Sheikh Jingir ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa da aka sanya a shafin Facebook ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Sheikh Jingir ya yi ƙarin bayani kan kalamansa da suka tayar da ƙura a Najeriya
Malamin ya ce matsayinsa ba shi da wata alaƙa da siyasa ko nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kamfen, illa dai ya samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin sauke nauyin da ke kansa a matsayinsa na Musulmi.
Ya ce zai ci gaba da goyon baya tare da ƙarfafa Musulmai su mara wa tikitin Musulmi da Musulmi baya, ko da kuwa hakan zai jawo masa suka.
“Zan ci gaba da goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi kuma zan ƙarfafa mutane su goya masa baya. Abin da za su faɗa ba zai hana ni ba." In ji shi
Jingir ya goyi bayan tikitin muslim-muslim
Malamin ya bayyana goyon bayansa ne yayin wani bikin auren jama’a da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya, inda aka aurar da ma’aurata 1,500.
A lokacin bikin, Jingir ya bayyana goyon bayan tsarin Musulmi da Musulmi, tare da kira ga Musulmai da su yi zaɓe ta yadda za su nuna irin ƙarfin adadinsu a Najeriya.
Jingir ya ce ya yanke shawarar goyon bayan tsarin ne bayan Shugaba Tinubu ya “ɗaga tutar” tikitin Musulmi da Musulmi.
Ya ƙara da cewa a matsayinsa na mai wa’azin Musulunci, yana da damar yin kira ga tsarin siyasa da ya yi daidai da abin da ya yi imani da shi a addininsa.
Ya yi magana kan yawan Musulmai
Malamin ya kuma ƙalubalanci ikirarin cewa Kiristoci ko wasu ƙungiyoyin addini sun fi Musulmai yawa a Najeriya, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Kalaman nasa sun ci gaba da jawo martani daga jama’a, inda wasu masu sharhi suka bayyana su a matsayin kalaman da za su iya raba kan al’umma, yayin da wasu suka kare hakkinsa na bayyana ra’ayinsa na addini da siyasa.
Wani masanin harkokin siyasa ya ce kalaman na iya ƙara ƙarfafa goyon bayan masu zaɓe Musulmai waɗanda suka mara wa tikitin Musulmi da Musulmi baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, gabanin zaɓen 2027.
Sai dai masanin ya yi gargaɗin cewa wannan matsayi na iya nisantar da wasu masu zaɓe waɗanda ba Musulmai ba, waɗanda a baya suka goyi bayan Shugaba Tinubu.

Source: Facebook
Lauya ya soki Sheikh Jingir
A wani labarin kuma, kun ji cewa Deji Adeyanju, ya yi Allah-wadai da kalaman da Sheikh Sani Yahya Jingir, ya yi na goyon bayan ci gaba da amfani da tikitin Musulmi-Musulmi.
Deji Adeyanju ya yi gargadin cewa kalaman addini da za su iya ƙara kawo rarrabuwar kawuna da za su iya barazana ga haɗin kan Najeriya.
Asali: Legit.ng
