An Kuma Ɗauko Batun da ka Iya Hana Shugaba Tinubu Komawa Mulki a Zaben 2027

An Kuma Ɗauko Batun da ka Iya Hana Shugaba Tinubu Komawa Mulki a Zaben 2027

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 21 ga Satumba, 2026 domin sauraron karar da aka shigar da Shugaba Tinubu
  • Kungiyar CFRPA ta nemi kotu ta hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsayawa takara a babban zaben 2027
  • Kungiyar ta zargi Tinubu da gabatar da takardun karatu na bogi da kuma takardar NYSC ta karya, lamarin da ta ce ya saba doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 21 ga Satumba, 2026 domin sauraron wata kara da ke neman a hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsayawa takara a zaben 2027 bisa zargin jabun takardun karatu.

Kungiyar Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA) ce ta shigar da karar, inda ta nemi kotu ta bayar da umarnin hana Tinubu shiga takarar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

Jami'ar ABU ta waiwayi Farfesa Abdullahi, wanda aka ce yana da PhD 5, MSc 5 da digiri 7

Tinubu.
Mai girma shugaban kasa, AsiwajubBola Ahmed Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa an shigar da karar ne bisa zargin cewa shugaban kasar ya gabatar da takardun karatu na bogi daga jami'ar Chicago da takardar shaidar kammala aikin yi wa kasa hidima ta NYSC ta karya ga INEC.

Yadda aka shigar da karar kan Tinubu

A karar mai lamba FHC/K/CS/312/2026, kungiyar CFRPA ta gabatar da bukatarta ga kotun, tana kalubalantar cancantar Tinubu na sake tsayawa takarar shugaban kasa.

Kungiyar ta yi zargin cewa takardun da aka gabatar wa INEC a lokacin zaben 2023 ba ingantattun takardu ba ne, tana mai neman kotu ta dauki matakin da zai hana shugaban kasar shiga zaben 2027.

Shugaba Tinubu ba shi kadai ne wanda aka hada a matsayin wanda ake kara ba, an kuma sanya Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Jami'ar Chicago University cikin wadanda ake kara a shari’ar.

Hakan na nufin kotun za ta saurari matsayinsu da kuma takardun da bangarorin suka gabatar kafin ta yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar mata, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya maka ADC kotu bayan rasa tikitin takarar gwamna

Kotu za ta fara zama kan karar

Kotun ta sanya ranar 21 ga Satumba domin zaman farko kan karar, wato zaman da kotu za ta duba matsayin shari’ar da kuma matakan da suka rage kafin a ci gaba da sauraron muhimman batutuwan da ke cikin karar.

Batun takardun karatun Tinubu da takardar NYSC ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce a harkokin siyasar Najeriya, musamman tun bayan zaben shugaban kasa na 2023.

Kotu.
Gudumar da amsu shari'a ke amfani da ita a zaman kotunan Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Sai dai a wannan karar da ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, kungiyar CFRPA ce ta sake gabatar da batun a gaban kotu tare da neman matakin shari’a kan shirin Shugaba Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu a 2027.

An yi wa Tinubu alƙawarin kuri'u a 2027

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya ce APC za ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027, tare da tabbatar wa Tinubu cikakken goyon baya.

Gwamna Kefas ya kuma yi alƙawarin cewa Taraba za ta samar da kuri’u ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC daga sama har ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262