Dan Takarar NDC: 'Abin da Ya Sa Najeriya ke Bukatar Obi da Kwankwaso'
- Ɗan takarar NDC na mazabar Ogoja/Yala a majalisa ya ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun fi sauran ‘yan takarar nagarta wajen jagorantar Najeriya
- Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke hasashen makomar shugaban kasa mai ci, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu game da zaben da duk jam'iyyu ke shirin fafatawa
- Peter Akah ya ce Najeriya na bukatar sauyin shugabanci da ingantaccen tsarin zaɓe domin kawo ƙarshen wasu daga cikin matsalolin da ake ciki a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ɗan takarar jam’iyyar NDC na kujerar Majalisar Wakilai ta tarayyar Ogoja/Yala a Cross River a zaɓen 2027, Peter Akah, ya bayyana nagartar yan yakarar da suka tsayar.
Ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, su ne suka fi cancanta su jagoranci Najeriya a halin yanzu.

Source: Twitter
Nigerian Tribune ruwaito cewa Akah ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kan takararsa, zaɓen 2027 da kuma yanayin siyasar ƙasar.
Da takarar NDC ya magantu
A hirar, Peter Akah ya ce Obi da Kwankwaso sun nuna ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati da kuma kula da albarkatun jama’a a lokacin da suke gwamnonin Anambra da Kano.
A kalamansa:
“Peter Obi da Rabiu Kwankwaso dama ce ga Najeriya ta fara samun waraka tare da dakatar da zubar jini."
Akah ya ce babbar matsalar Najeriya ba rashin albarkatu ba ce, sai dai cin hanci da rashawa da rashin ɗaukar alhaki. Ya zargi wasu masu rike da mukaman gwamnati da karkatar da dukiyar ƙasa.
Ana NDC za ta warkar da Najeriya
Dan takarar majalisar tarayyar ya kuma ce tikitin Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai bai wa ‘yan Najeriya wata madadin tsarin mulkin da ake ciki.
Dan takarar NDC ɗin ya kuma soki matakin Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na daskarar da asusun gwamnatin Jihar Osun, yana mai cewa hakan na iya yin tasiri kan tsarin zaɓen gwamnan jihar.

Source: Facebook
Ya yi tambaya kan dalilin da ya sa aka ɗauki matakin a wannan lokaci, yana mai cewa idan ana son binciken yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, ya kamata a gudanar da irin wannan bincike a jihohi daban-daban.
Akah ya ce:
“EFCC ba za ta iya farkawa wata rana ta yanke shawarar daskarar da asusun gwamnatin jiha kwanaki kaɗan kafin zaɓe da sunan wai bincike."
Wuta ta taso a jam'iyyar NDC
A baya, kun samu labarin cewa Muhammad Rabiu Bakin Zuwo ya yi bayanin wasu daga cikin abubuwan da suka rika faruwa a cikin jam’iyyarsu ta NDC wanda wasu ke ganin an yi masu ba dai-dai ba.
Shugaban jam’iyyar ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da murkushe su da hana mutanensa samun takara duk da cewa sun shigo cikin NDC daga baya domin kowa ya samu mafita gabanin zaben 2027.
Muhammad Bakin Zuwo ya ce jagoran na Kwankwsiyya ya dage sai ya raba shi Usaini Mai Riga daga mukamansu a Kano, kuma zargin ya zo bayan wani zama da aka taba yi a baya domin warware dambarwar.
Asali: Legit.ng

