"Ba Tinubu Na Ke Tallatawa ba"; Sheikh Jingir Ya Fadi Dalilin Tallar Muslim Muslim
- Kalaman da sanannen malamin addinin Musulunci Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi amfani da su wajen tallata tikitin muslim-muslim na ci gaba da jawo cece-kuce
- Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa yana da 'yancin ya zabi abin da yake so da abin da ya kwanta masa a rai domin ra'ayinsa ne
- Sheikh Jingir ya bayyana cewa ba Shugaba Bola Tinubu yake tallatawa ba, duk da kiran da yake yi na azabi tikitin muslim-muslim
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jos, jihar Plateau - Sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske kan goyon bayansa ga tikitin muslim-muslim.
Sheikh Jingir ya bayyana cewaya daɗe yana goyon bayan a samu shugaban ƙasa musulmi kuma mataimakinsa musulmi, tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar BBC Hausa, a ranar Talata, 11 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
"Kiristanci na cikin matsala"; Malamin addini ya dauki zafi kan kalaman Sheikh Jingir
A yayin hirar, malamin ya yi bayani kan kalaman da ya yi game da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa wadanda suka jawo cece-kuce.
Kalaman dai na Sheikh Jingir sun janyo zazzafar muhawara bayan da ya bayyana matsayarsa kan tikitin muslim-muslim.
Shin Sheikh Jingir yana tallata Tinubu?
A yayin hirar an tambayi Sheikh Jingir ribar da ya samu wajen ci gaba da tallata Shugaba Bola Tinubu, sai ya kada baki ya ce:
"Ni ba Tinubu na ke tallatawa ba, musulunci na ke tallatawa. Na ce maka musulunci na ba ta Tinubu ba ce, ba ta Buhari ba ce, ba ta wani dan Adam ba ce, ta ubangiji na Allah ce."
Hakazalika ya bayyana cewa kalaman na sa babu wanda zai tunzura domin ra'ayinsa yake fada.
"Aa ni bayanai babu wani abin da zai tunzura kowa. In ce maka kana da dama ka zabi abin da kake so, nima ina da dama in zabi abin da nake so, meye na tunzuri? Sai dai idan jahilci ne zan yi ta nanatawa har a gane."

Kara karanta wannan
Sheikh Jingir ya sake fadar abin da masu sukarsa kan muslim muslim ba za su so ba
Sheikh Jingir ya ce yana da 'yanci
Malamin addinin ya bayyana cewa yana da 'yancin ya zabi abin da yake so, kuma yana da 'yancin ya tallata musulunci.
Tun gabanin babban zaɓen shekarar 2023, Sheikh Yahaya Jingir ya ja hankalin al’umma bayan ya fito karara ya ayyana goyon bayansa kan takarar Bola Tinubu, bayan da ya ɗauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.
Malamin addinin musuluncin ya ce ya nace kan wannan batu ne saboda abin da addini ya koyar na cewa “Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne”.

Source: Facebook
Primate Ayodele ya ragargaji Sheikh Jingir
A wani labarin kuma, kun ji cewa Primate Elijah Babatunde Ayodele da ke shugabantar cocin INRI Evangelical Spiritual, ya soki Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kalaman da ya yi.
Primate Ayodele ya ce ya kamata a kama Jingir kan kalaman, yana gargadin cewa rashin daukar mataki kan shugabannin addini da ke yin kalaman tayar da hankali na iya yin barazana ga zaman lafiya da zaman tare a Najeriya.
Asali: Legit.ng