Gwamnati Ta Fadi Kalubalen da Kano Ke Fuskanta, Ta Nemi Taimakon Tarayyar Turai
- Gwamnatin Kano ta nemi taimakon Tarayyar Turai kan ci gaban birane da tattalin arziki da zai kyautata rayuwar al'ummar jihar
- Mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo, ya ce Kano na fuskantar kalubalen karuwar jama’a da matsin lamba kan ababen more rayuwa
- Jakadan EU a Najeriya ya bayyana dalilin da ya sa kungiyar ta zabi Kano yayin da ya ce yi tsoka kan matsayinta a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Gwamnatin Kano ta bukaci hadin gwiwa da Tarayyar Turai (EU) a muhimman fannoni domin inganta ci gaban birane da kyautata rayuwar al’ummar jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da jakadun Tarayyar Turai da wakilan kasashe takwas mambobin kungiyar da suka kai ziyara Kano.

Source: Twitter
Kano ta nemi taimakon Tarayyar Turai

Kara karanta wannan
"Sau 3 kacal na ga ƴaƴana," Zulum ya tuno abin da ya faru da shi bayan zaben 2019
Murtala Garo, wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce ziyarar ta ba gwamnatin jihar damar bayyana manufofinta na bunkasa birane tare da jawo karin hadin gwiwa daga kasashen ketare, in ji Channels TV.
Ya bayyana Kano a matsayin daya daga cikin tsoffin cibiyoyin kasuwanci mafi girma da saurin bunkasa a nahiyar Afrika.
A cewarsa, karuwar jama’a da fadada birane na haifar da matsin lamba kan ababen more rayuwa kamar gidaje, hanyoyi, sufuri, tsaftar muhalli da kula da yanayi.
“Saboda haka muna bukatar sababbin dabaru da hadin gwiwa domin shawo kan wadannan kalubale,” in ji Garo.
Kano ta bayyana sabon kundin ci gaba
Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin Kano ta samar da wani cikakken kundin tsarin bunkasa birane domin tabbatar da cigaba mai tsari da dorewa.
Ya ce manufar wannan kundi ta kunshi inganta tsarin gine-gine, samar da ingantattun ababen more rayuwa, bunkasa tattalin arziki, kare muhalli da amfani da fasahar zamani.
Jaridar Punch ta rahoto Garo ya kara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin tarayya da kuma muradun ci gaba masu dorewa na duniya.
Ya bukaci Tarayyar Turai ta tallafa wa Kano a fannoni kamar ilimi, horar da matasa sana’o’i, noma, lafiya, makamashi mai sabuntawa da sadarwar zamani.
Haka kuma ya nemi taimakon fasaha wajen duba dokar hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin jawo karin masu zuba jari.

Source: Twitter
Jakadan EU ya yabawa Kano
A nasa bangaren, jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Gautier Mignot, ya bayyana Kano a matsayin muhimmiyar cibiyar ci gaba a Arewacin Najeriya.
Ya ce zaben Kano a matsayin daya daga cikin wuraren da tawagar ta ziyarta ya nuna irin muhimmancin da kungiyar ke bai wa jihar a dangantakarta da Najeriya.
Mignot ya bayyana cewa ziyarar na daga cikin shirin EU na kara karfafa hadin gwiwa da yankuna daban-daban na Najeriya.
EU ta goyi bayan farfado da Kano
A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da sabuwar cibiyar kirkire-kirkire ga mata a Kano domin tallafa wa ‘yan kasuwa.
An ce cibiyar za ta taimaka wajen farfado da tsohuwar masana’antar yadi ta Kano ta hanyar fasaha, kirkire-kirkire da tsarin kasuwanci na zamani.
Gwamnatin Kano ta goyi bayan shirin tana mai cewa ci gaban mata a fannoni kamar fasahar zamani babbar hanya ce ta gina makomar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
