Kwana Ya Kare: An Hallaka Mawaki dan Asalin Najeriya a Burtaniya

Kwana Ya Kare: An Hallaka Mawaki dan Asalin Najeriya a Burtaniya

  • Ajali ya riski wani mawaki dan asalin Najeriya a kasar Burtaniya bayan da aka caka masa wukar da ta yi sanadiyyar mutuwarsa
  • Mark Yinka Orabiyi ya kasance shahararren mawaki wanda ya yi aiki da manyan mawaka lokacin da yake raye
  • Iyalansa sun fitar da sanarwar da ke tabbatar da mutuwarsa, inda suka bayyana rashinsa a matsayin abin bakin ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Landan, Burtaniya - Mark Yinka Orabiyi, mawaƙi kuma marubucin waƙoƙi ɗan asalin Najeriya wanda aka fi sani da sunan Talay Riley, ya rasa ransa a Burtaniya.

Mawakin ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 35 bayan da aka soka masa wuƙa a Gabashin birnin Landan.

An kashe Taley Riley a Burtaniya
Mawaki Taley Riley da aka hallaka a birnin Landan Hoto: Randall Michelson
Source: Getty Images

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar Jumma'a a kan titin Pankhurst Avenue da ke Silvertown, kamar yaddda kafar yaɗa labarai ta yankin, Newham Recorder, ta bayyana.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta yi magana game da ƙorafin Kwankwaso da barazanar zai bar NDC

An kira jami'an ba da agajin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru, amma ba a samu nasarar ceto ran mawaƙin wanda ya taɓa lashe kyautar Grammy ba.

Jami'an binciken kisan kai daga sashin binciken manyan laifuffuka na musamman sun ƙaddamar da binciken kisan kai kan lamarin.

Iyalan Taley Riley sun fitar da sanarwa

An kuma tabbatar da mutuwar Talay a cikin wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Sun siffanta rashin nasa a matsayin “baƙin ciki mai girman gaske.”

Iyalan sun tuna da Riley ba wai kawai don nasarorin da ya samu a fagen aikinsa ba, har ma da kyawun halayensa.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Cikin tsananin baƙin ciki muke tabbatar da cewa Mark ‘Yinka’ Orabiyi, wanda aka fi sani da Talay Riley a fagen kwarewa, ya rasu a jiya da safe."
“Wadanda suka san shi a idon duniya za su ci gaba da tunawa da Talay saboda gagarumar fasaharsa a matsayinsa na marubucin waƙoƙi kuma mawaƙi da ya lashe kyautar Grammy kuma ya sayar da waƙoƙi da dama.”
“Ga waɗanda suka san shi kuma suka nuna masa ƙauna, barkwancinsa, karamcinsa, da kuma kasancewarsa ta musamman da ba ta ɓoyuwa su ne abubuwan da za a fi rashinsu.”

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Trump ya ki goyon bayan Isra'ila, ya gargadi Netanyahu da Khamenei

Iyalansu sun kuma nuna godiya ga goyon bayan da al'umma suka nuna musu biyo bayan wannan babban rashi.

An kashe mawaki Taley Riley a Burtaniya
Mawaki Taley Riley da aka kashe a Burtaniya Hoto: C Brandon
Source: Getty Images

Taley Riley ya yi suna kafin mutuwarsa

Talay, wanda ɗan'uwa ne ga mai shirya kiɗa Scribz Riley, ya shafe fiye da shekaru 10 yana canza fasalin salon kiɗa da waƙa na R&B.

Jaridar TheCable ta ce ya fara shiga cikin harkar ne yana ɗan shekara 18 bayan ya sanya hannu kan yarjejeniyar wallafe-wallafe da kamfanin Global Publishing.

Aikin sa ya samu gagarumin ci gaba bayan ya fito a cikin zaɓaɓɓiyar waƙar mawaƙi Chipmunk ta shekarar 2009, wanda hakan ya biyo bayan sanya hannu da ya yi da kamfanin Jive/Sony Records.

A cikin shekaru da dama, ya gudanar da rangadin rera waƙoƙi a ƙasashen Ingila (UK) da Amurka (US) tare da mawaƙa irin su Skepta, Usher, da Trey Songz, sannan ya yi haɗin gwiwa da Kehlani, H.E.R., Khalid, da kuma shahararriyar ƙungiyar Amurka ta 2BYG.

Tsohon shugaban Unilorin ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jami’ar tarayya ta Ilorin (Unilorin), Farfesa AbdulGaniyu Ambali, ya yi bankwana da duniya.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

Fitaccen masanin ilimin dabbobi kuma gogaggen malamin jami’a ya rasu ne da sanyin safiya a gidansa da ke Oloje Estate a Ilorin, jihar Kwara.

Majiyoyi daga iyalinsa sun bayyana cewa Ambali ya rasu da misalin karfe 3:00, ‘yan sa’o’i bayan ya halarci sallar Isha’i a wani masallaci da ke kusa da gidansa a daren Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng