Matsalar Tsaro: NLC da TUC Sun Yi Barazanar Hana Ma'aikata zuwa Wurin Aiki a Najeriya

Matsalar Tsaro: NLC da TUC Sun Yi Barazanar Hana Ma'aikata zuwa Wurin Aiki a Najeriya

  • Manyan kungiyoyin kwadago watau NLC da TUC sun ce rashin tsaro ya zama babbar barazana ga ma’aikata da tattalin arzikin Najeriya
  • Sun gargadi gwamnatin tarayya da cewa za su iya umartar ma’aikata su zauna a gida idan kashe-kashe da garkuwa da mutane suka ci gaba
  • Shugabannin kwadagon na Najeriya sun ce kusan mutum 2,000 aka kashe a watanni ukun farko na shekarar 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Geneva - Kungiyoyin kwadago mafi girma a Najeriya, NLC da TUC sun yi barazanar daukar matakai masu tsauri idan ba a dakile yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro ba.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, da mataimakin shugaban TUC, Oyibo Jimoh, ne suka bayyana hakan a taron yan kwadago na duniya (ILC) da ake yi a birnin Geneva da ke kasar Switzerland.

Kara karanta wannan

Lamari ya munana, malamin addini ya taso Tinubu a gaba ya yi murabus kan tsaro

Shugabannin kwadago.
Shuganannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a taron ranar ma'aikata ta duniya Hoto: NLC Nigeria
Source: Twitter

NLC ta koka kan rashin tsaron Najeriya

A rahoton Vanguard, kungiyoyin sun ce matsalar tsaro ta kai wani mataki mai hadari, inda ma’aikata a sassa daban-daban na kasar ke fuskantar barazanar rasa rayukansu yayin zuwa aiki.

A cewarsu, manoma suna tserewa daga gonakinsu, malamai na fuskantar hare-hare da garkuwa da su, yayin da ma’aikatan lafiya ke fuskantar farmaki a wuraren aiki.

“Yanzu ma’aikata suna sanya rayuwarsu cikin hadari domin kawai su je wurin aiki. Wannan matsala ce da ke barazana ga rayuwar jama'a da ci gaban kasa,” in ji NLC da TUC.

Sun nuna damuwa cewa duk da alkawuran gwamnatin tarayya, hare-hare da tashe-tashen hankula na ci gaba da yaduwa a sassa daban-daban na Najeriya.

Kungiyoyin sun ce bayanai sun nuna kusan mutane 2,000 aka kashe a watanni ukun farko na shekarar 2026, yayin da miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu sakamakon matsalolin tsaro.

Matakin da NLC da TUC suka shirya dauka

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

NLC da TUC sun bayyana cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalar cikin gaggawa, za su iya umartar ma’aikata su zauna a gidajensu domin kare rayukansu.

“Idan wannan hali ya ci gaba, za mu iya ba wa mambobinmu shawarar su daina zuwa aiki. Ba yajin aiki ba ne, illa matakin kare kai da rayuwa,” in ji su.

Sun kuma bayyana cewa kungiyar malaman makarantu ta ksa (NUT) ta riga ta fara daukar wasu matakan kariya a wuraren da matsalar tsaro ta fi kamari.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da baki a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

NCL ta nuna damuwa kan matsin rayuwa

Baya ga matsalar tsaro, kungiyoyin sun ce talauci da tsadar rayuwa na kara tsananta a kasar. Sun yi zargin cewa kusan kashi 65 cikin 100 na 'yan Najeriya, kimanin mutum miliyan 150, na rayuwa cikin talauci.

A cewarsu, karin farashin abinci, sufuri, gidaje da kiwon lafiya ya rage karfin albashin ma’aikata sosai, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Sun bukaci gwamnati ta kira tattaunawa ta kasa domin nemo hanyoyin warware matsalolin tsaro da kuma matsin rayuwa da ke addabar al’ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara ɗaukar mataki kan rashin tsaro, ana son samar da yan sandan jihohi

NlC ta yi fatali da tayin albashin N100,000

An ji cewa kungiyar NLC ta yi fatali da tayin N100,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi na ma'aikatan gwamnati a Najeriya.

NLC ta bayyana cewa tayin mafi ƙarancin albashi na N100,000 da wasu gwamnoni suka yi bai dace da halin da ma’aikatan ƙasar ke ciki ba.

Ta ce ma'aikata sun cancanci a ba su albashin da bai gaza Naira miliyan 1 ba duba da matsin rayuwar da ake ciki bayan cire tallafin mai da faduwar darajar Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262