Takaitaccen tarihin Peter Obi, wanda Atiku ya zaba yayi masa mataimaki a zaben 2019

Takaitaccen tarihin Peter Obi, wanda Atiku ya zaba yayi masa mataimaki a zaben 2019

Da yammacin ranar Juma'a ne dai muka samu labarin cewa Atiku Abubakar wanda ya lashe zaben fitar da gwani sannan kuma ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zabe mai zuwa ya zabi Peter Obi a matsayin mataimakin sa.

Wannan ne ma ya sanya muka nemo maku dan takaitaccen tarihin na Peter Obi domin ilmantar da ku game da sanin ko waye shi.

Takaitaccen tarihin Peter Obi, wanda Atiku ya zaba yayi masa mataimaki a zaben 2019
Takaitaccen tarihin Peter Obi, wanda Atiku ya zaba yayi masa mataimaki a zaben 2019
Asali: Twitter

KU KARANTA: Aikin ginin sabuwar matatar mai zai kankama a Najeriya

Shi dai Peter Obi an haife shi ne a ranar 19 ga watan Yuli, shekara ta 1961 a garin Onitsha, jihar Anambra inda kuma yayi karatun sa na Furamare da Sakandare.

Daga nan ne kuma sai ya tafi jami'ar Nsukka a shekarar 1980 a jihar Enugu inda a nan yayi karatun sa na digiri na farko a fannin tunani da kuma halayyar dan adam.

Haka zalika bayan nan ne sai ya koma makaranta domin yin karatun kasuwanci na zamani saboda sha'awar da yake da ita a fannin kamar dai yadda ya fada a cikin wata firar sa da yayi da manema labarai.

Peter Obi kafin shigar sa siyasa attajiri ne sosai inda ya kafa kamfanoni da dama kafin daga bisani ya zama shugaban bankin Fidelity mafi karancin shekaru.

Ya kuma rike mukamin gwamnan jihar Anambra na wa'adin shekaru 8 a wani yanayi mai cike da sarkakkiya da dambarwar siyasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel