Kwankwaso Ya Fusata kan Rashin Tsaro, Ya Ragargaji Tinubu

Kwankwaso Ya Fusata kan Rashin Tsaro, Ya Ragargaji Tinubu

  • 'Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki gwamnatin Najeriya kan rashin kawo ƙarshen matsalar tsaro
  • Kwankwaso, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya nuna damuwa kan hare-haren da ya ce ‘yan ta’adda ke kai wa a jihohin Zamfara, Borno da sauransu
  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa fashi da makami, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, ta’addanci sun zama ruwan dare a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron Najeriya cikin gaggawa.

Ya yi magana yana mai gargadin cewa rashin tsaro na ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar duk da makudan kuɗi da ake kashewa a fannin.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta yi magana game da ƙorafin Kwankwaso da barazanar zai bar NDC

Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso yayin wani bayani a gidan shi da ke Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, ya ce ƙaruwar matsalar rashin tsaro a jihohi da dama ya sa ’yan Najeriya da yawa ke rayuwa cikin tsoro.

Korafin Rabiu Kwankwaso kan tsaro

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce fashi da makami, garkuwa da mutane, ta’addanci, rikice-rikice da kuma fashin makami sun zama ruwan dare a kasar nan.

“Cikin damuwa, na lura da yadda rashin tsaro ya mamaye ƙasarmu. Ana zubar da jini sosai a kasar nan,”

In ji shi.

Tsohon gwamnan ya lissafo jihohin Zamfara, Borno, Sokoto, Katsina, Kwara da Oyo a cikin wuraren da rikicin ya shafa, yana mai nuna takaicinsa cewa ’yan ƙasa da yawa ba za su iya kwana cikin kwanciyar hankali.

Za a iya magance matsalar tsaro

Lura da gogewarsa a matsayin tsohon gwamna kuma ministan tsaro, Kwankwaso ya ce kalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta ba wani abu ne da ba za a iya shawo kansa ba.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya

“A matsayina na wanda ya yi wa wannan ƙasa hidima a matakai daban-daban, ciki har da matsayin gwamnan jihar Kano da kuma ministan tsaro, inda muka fuskanci kuma muka rage matsalolin tsaro sosai ta hanyar jagoranci mai ƙarfi da haɗin gwiwar al’umma, har yanzu na yi imanin cewa rashin tsaro ba abu ne da ya fi ƙarfin magani ba,”
Wasu 'yan daba da aka kama a Kano
Yadda aka kama wasu masu aikata laifuffuka a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa ya ce matsalar ƙasar ba rashin albarkatu ba ce, sai dai rashin himmar shugabannin siyasa domin tinkarar rashin tsaro yadda ya kamata.

Kwankwaso ya yi kira da a inganta jin daɗi da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, da ƙara tattara bayanan sirri, da bunƙasa aikin ’yan sandan al’umma, tare da ɗaukar matakan magance tushen matsalar rashin tsaro.

Kwankwaso na nan a NDC

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana nan a jam'iyyar NDC duk da rade-radin zai sauya sheka da ake.

A wata hira da ya yi, Kwankwaso ya sanar da cewa yana tare da Peter Obi kuma za su yi takara a zaben 2027 tare domin ciyar da Najeriya gaba.

Tsohon gwamnan ya yi magana kan takarar sanata da suka ba tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna a jam'iyyar NDC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng