2027: Tsohon Shugaban Kasa, Obasanjo Ya Gana da Jagororin Tafiyar Obi da Kwankwaso

2027: Tsohon Shugaban Kasa, Obasanjo Ya Gana da Jagororin Tafiyar Obi da Kwankwaso

  • Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya gana da shugabannin tafiyar Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso (OK Movement)
  • Cif Obasanjo da yan siyasar sun tattauna kan hadin kan kasa da kuma bunkasa siyasar da ta fi mayar da hankali ga talakawa
  • Jigon NDC, Ladipo Johnson, ya ce ganawar za ta kara karfafa manufofin kungiyar yayin da suke tunkarar babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya gana da shugabannin tafiyar dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Sanata Rabiu Kwankwaso (OK Movement).

Ana ganin dai wannan ganawa wani mataki ne daga cikin kokarin hada kan 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki domin gina makomar Najeriya.

Tsohon shugaban kasa, Obasanjo.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yana magana a wurin taro Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook

Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar NDC kuma mamba a tafiyar Obi-Kwankwaso, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan bayan ganawar, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Me kuma suke so"; Ana neman tunzura jagoran NDC kan tikitin Obi da Kwankwaso a 2027

Abin da OK suka tattauna da Olusegun Obasanjo

Johnson ya bayyana cewa ganawar ta kasance mai muhimmanci kuma ta mayar da hankali ne kan yadda za a kara hada kan 'yan Najeriya tare da inganta manufofin da suka shafi jin dadin jama'a.

A cewarsa, Obasanjo ya bayar da shawarwari da darussa masu amfani daga kwarewarsa ta shugabanci da hidimar kasa, wadanda za su taimaka wajen karfafa tafiyar.

Ya ce:

"Tafiyar OK Movement ta gudanar da muhimmiyar ganawa da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo domin sake jaddada kudurinmu na gina Najeriya mai karfi, hadin kai da ci gaba."

'Yan OK sun yaba da kwarewar Obasanjo

Johnson ya kara da cewa hikima, gogewa da fahimtar shugabanci da Obasanjo ya raba musu za su taimaka wajen kara kuzari da karfafa kokarin kungiyar na gina tafiya mai mayar da hankali kan muradun jama'a.

Ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da hada kan 'yan Najeriya tare da karfafa goyon bayan masu neman sabuwar Najeriya domin samar da ci gaba da walwala ga kowa, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

2027: Takarar Kwankwaso da Obi ta sake samun karfi, dattawa sun mara masu baya

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye da tattaunawa tsakanin manyan 'yan adawa da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a tsara siyasar Najeriya gabanin zabukan da ke tafe.

Tsohon shugaban kasa.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo tare da jagororin tafiyar Obi/Kwankwaso Hoto: Mubarak Salisu
Source: Facebook

Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanan abin da aka tattauna ba, ana ganin cewa ganawar ta nuna karin kusanci da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki da ke da alaka da tafiyar Obi-Kwankwaso da sauran fitattun jagororin kasa.

Johnson ya nuna kwarin gwiwa game da makomar Najeriya, inda ya sake jaddada taken tafiyar cewa:

"Najeriya za ta kasance lafiya kuma za ta yi nasara."

Obasanjo ya nemi hadin kan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ɗauki alhakin gina makomar ƙasar baki ɗaya.

Obasanjo ya yi gargaɗin cewa samun ci gaba mai ma’ana zai ci gaba da kasancewa abu mai wahala har sai idan ’yan Najeriya sun haɗa kai don magance ƙalubalen ƙasar.

Haka zalika, ya jaddada buƙatar sanya matasa dumu-dumu a cikin harkokin mulki da hanyoyin ci gaba, inda ya bayyana su a matsayin jigon makomar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262