Buhari ya tuno tsohuwar alaka, ya rabawa iyalin abokansa da suka mutu mukamai a NNPC

Buhari ya tuno tsohuwar alaka, ya rabawa iyalin abokansa da suka mutu mukamai a NNPC

  • FCT, Abuja - Wasu daga cikin wadanda aka nada domin su rika kula da aikin kamfanin NNPC, na-kusa ko manyan na hannun daman shugaban kasa ne
  • Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto, inda ta bayyana yadda Mai girma Muhammadu Buhari ya tuna da dangin mutanen da suka dade tare da shi a siyasa.
  • Za a gane hakan ganin yadda aka maye gurbin Sanata Ifeanyi Ararume da Lady Margaret Okadigbo, matar abokin tafiyar Buhari a lokacin hamayya

Iyalin Okadigbo

A lokacin da Muhammadu Buhari ya fara takarar shugaban kasa a zaben 2003, Marigayi Chuba Okadigbo ne ya tsaya masa a matsayin mataimaki a APP.

A wannan shekara ne Sanata Chuba Okadigbo ya rasu. Shekaru fiye da 10 da mutuwarsa sai Buhari ya ba matar da ya bari, Margaret Okadigbo kujera a NNPC.

Kara karanta wannan

Mai dakin Buhari ta canza masu rayuwa, tayi wa masu nakasa hanyar samun aiki mai-tsoka

'Yar Harry Marshal

Gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta manta da iyalan Sarkin yakinsa, Harry Marshal ba. A makon nan aka ba ‘yarsa, Constance Harry Marshal esq mukami.

Iyalin Umar

Kamar yadda rahoton ya bayyana, wani gida da Buhari ya tuna da hau mulki shi ne gidan Umar. Tun tuni Shugaban kasar ya ba Tajudeen Umar mukami a NNPC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron IATF
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: MuhammaduBuhari
Asali: Facebook

Obih - mutumin Amaechi

Injiniya Henry Ikemefuna Obih wanda yana cikin wadanda aka ba kujera a NNPC, na-kusa da Rotimi Amaechi, wanda yana cikin kusoshi a gwamnatin APC.

Akinyelure ya samu matsayi

Cif Pius Akinyelure ya taba rike mataimakin shugaban jam’iyyar APC a kudu maso yamma. Ganin yanzu ba ya majalisa, aka sa shi a majalisar da ke sa ido a NNPC.

Bobboi Ahmed

Tun a 2016 aka ba Bobboi Ahmed mukami a ma’aikatar PEF ta kasa. Duk da an ruguza wannan hukuma. Shugaban kasar bai manta da yaron tsohon amininsa ba.

Kara karanta wannan

Doyin Salami: Abubuwa 12 da ya dace a sani game da masanin da zai ceto tattalin Najeriya

Aisha Buhari tayi kokari

Uwargidar Shugaban kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta yi amfani da damar ta, ta nemawa wasu Bayin Allah hanyar da za su samu abinci a gwamnati.

An ji cewa ganin su na dauke da nakasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta ba mutane biyu aiki a ma'aikatar NSITF bayan sun kammala bautar kasa watau NYSC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel