PDP Ta Yi Sabon Ango, Dan Majalisa a Kano Ya Watsar da Jam'iyyar Abba Kabir

PDP Ta Yi Sabon Ango, Dan Majalisa a Kano Ya Watsar da Jam'iyyar Abba Kabir

  • Dan majalisar Kano mai wakiltar Tudun Wada ya fice daga APC ya koma PDP bayan shawarwari da magoya baya da iyalansa
  • Bayan ficewarsa, Majalisar Dokokin Kano mai mambobi 40 har yanzu tana da mafi yawan ’yan majalisa daga APC har 37
  • Dan siyasar ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne bisa ra’ayinsa, bayan dogon tunani da tuntubar abokan siyasa, magoya baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Tudun Wada a Majalisar Dokokin Kano ya yi murabus daga jam’iyyar APC tare da komawa PDP.

Bayan sauya shekar, Majalisar Dokokin Kano mai mambobi 40 yanzu tana da ’yan majalisa 37 na APC, biyu na NNPP da guda ɗaya na PDP.

Dan majalisar Kano ya fice daga APC
Gwamna Abba Kabir da Hon. Sule Lawan Shuwaki. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Sani Auwal.
Source: Facebook

Dan majalisar Kano ya bar APC

Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ne ya karanta wasikar murabus din Sule Lawan Shuwaki yayin zaman majalisar na ranar Litinin, cewar Tribune.

A cikin wasikar, dan majalisar ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntubar abokan siyasarsa, magoya bayansa da iyalansa, tare da yin dogon nazari kan matakin.

Shuwaki ya nuna godiyarsa ga shugabannin APC daga matakin unguwa, karamar hukuma, jiha da kasa bisa damar da goyon bayan da ya samu yayin kasancewarsa cikin jam’iyyar.

Sai dai ya ce ya zabi wata sabuwar hanyar siyasa ne bisa abin da ya yi imani da shi da kuma ra’ayinsa na kashin kansa.

Bayan karanta wasikar, Kakakin Majalisar Falgore ya bukaci Shuwaki ya tabbatar da cewa shi da kansa ne ya mika wasikar murabus din ga majalisar.

Shuwaki ya tabbatar da cewa ya yi murabus daga APC tare da komawa PDP, yana mai cewa ya shiga PDP tun watanni da suka gabata.

Sai dai ya bayyana cewa shawarwari da aka yi kan makomar siyasarsa ne suka jinkirta gabatar da wasikar murabus din a hukumance.

APC ta rasa dan majalisa a Kano
Taswirar jihar Kano da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Shuwaki ya tuna magoya bayansa

Dan majalisar ya kuma gode wa tsofaffin abokan siyasarsa da magoya bayansa a Tudun Wada bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ganin ya zama dan majalisar.

Ya bukaci jama’a da su ci gaba da karfafa hadin kai da kyakkyawar mu’amala duk da bambance-bambancen siyasa da ke tsakaninsu.

Falgore ya bayyana cewa Majalisar ta karbi wasikar murabus din Shuwaki kimanin watanni biyu da suka gabata, amma aka jinkirta gabatar da ita.

Ya ce an yi hakan ne bayan shawarwari da dan majalisar domin tantance ko zai ci gaba da matsayar da ya dauka na barin APC, cewar Daily Post.

Rikici ya barke tsakanin APC, Dan Bilki

An ji cewa Dan Bilki Kwamanda ya yi watsi da sanarwar da shugabannin APC na Kano suka yi kan dakatar da shi daga jam’iyyar, yana mai cewa babu wanda ya isa ya kore shi.

Kwamanda ya ce ya shiga APC ne da ra’ayinsa kuma ba ya tsoron fuskantar abokan hamayyarsa, yana mai cewa zai cigaba da fadin ra’ayinsa kan abubuwan da suka shafi jam'iyyar.

Ya kuma caccaki shugabannin APC na Kano kan abin da ya kira rashin mayar da hankali kan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar da nema mata mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.