Kwankwasiyya Ta Yi Magana game da Ƙorafin Kwankwaso da Barazanar zai Bar NDC

Kwankwasiyya Ta Yi Magana game da Ƙorafin Kwankwaso da Barazanar zai Bar NDC

  • Ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi martani ga rahotannin da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na son barin NDC
  • Kakakin ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya bayyana zuwa yanzu, Kwankwaso bai mika wani koke ga uwar jam'iyya ba
  • Ya ce an gudanar da zaɓen fitar da gwani bisa doka kuma akwai kuskure a rahoton da ake yada wa kan zargin akwai baraka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu matsala da NDC.

Haka kuma kungiyar ta ce babu wata barazanar ficewa daga NDC da ya yi sakamakon sauya sunayen wasu ƴan takarar jam'iyyar a zaben 2027.

Kwankwasiyya ta magantu game da rikici da NDC
Peter Obi, Seriake Dickson da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa kakakin ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya bayyana rahotannin a matsayin jita-jita marasa tushe a hira da manema labarai a ranar Litinin, 9 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

Martanin Kwankwasiyya kan shirin barin NDC

The Guardian ta kawo labarin cewa Ƙungiyar Kwankwasiyya za ta iya ficewa daga NDC idan aka cire wasu daga cikin magoya bayanta da aka tsayar takara.

Lamarin ya biyo bayan sauya sunayen wasu ƴan takarar da ƙungiyar ta gabatar, lamarin da ya haifar da zarge-zargen cewa an karya wata yarjejeniyar raba madafun iko da aka cimma a baya.

Sai dai Habin Mohammed ya ce babu wani sahihin dalili da zai nuna cewa Kwankwasiyya na fushi ko kuma tana shirin ɗaukar wani mataki kan lamarin.

Kwankwaso ba shi da matsala da NDC - Kwankwasiyya

A cewarsa, babu wani ƙorafi daga Kwankwaso ko kuma daga Ƙungiyar Kwankwasiyya dangane da batun sauya sunayen ƴan takara.

Kwankwasiyya ta ce Sanata Kwankwaso bai ce zai bar NDC ba
Jagoran darikar Kwankwasiyya na Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya ce:

"Ƙungiyar Kwankwasiyya, haka kuma jagoranta, ba su nuna wata damuwa kan lamarin ba."

Mohammed ya ƙara da cewa an gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar a ranar 29 ga Mayu, 2026 bisa tanadin dokar zaɓe da kuma ƙa'idojin hukumar INEC.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An fara shirin hana jam'iyyar su Kwankwaso shiga zaben 2027

Kakakin ya bayyana cewa tun kafin gudanar da zaɓukan, shugabanni da sauran 'yan NDC sun amince da amfani da tsarin maslaha.

Ya ce bayan cimma matsayar, an tantance ƴan takarar da aka amince da su tare da miƙa sunayensu ba tare da wata matsala ko saɓani a cikin jam'iyyar ba.

Habib Mohammed ya kuma bayyana cewa har zuwa yanzu Kwankwaso bai sanar da Ƙungiyar Kwankwasiyya wata damuwa ko rashin jin daɗi da yake da ita game da jam'iyyar ba.

Ya ce jam'iyyar NDC ce ta fi dacewa ta yi cikakken bayani kan rahotannin da ke cewa akwai sabani da Kwankwasiyya.

Ana rade-radin Kwankwaso zai iya barin NDC

A baya, mun kawo labarin cewa bisa ga dukkannin alamu abubuwa na neman tabarbarewa tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da shugabannin NDC a Najeriya.

An ruwaito cewa shugabannin na NDC sun sauya sunaye wasu 'yan takara cikin 'yan Kwankwasiyya domin mutunta yarjejeniyar da aka yi da Kwankwaso a baya.

Sai dai, alamu sun nuna hakan bai yi wa madugun darikar Kwankwasiyya dadi ba, inda ya yi baranazar raba gari da jam'iyyar adawar duk da yadda babban zabe ke tunkarowa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng