Hudubar da Sarkin Musulmi Ya Yi wa Musulmai da Kiristocin Najeriya
- Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya buƙaci Musulmi da Kiristoci su daina aibanta addinan juna
- Mai alfarma Sultan ya gargadi mabiya addinai da kada wani bangare ya dauki kansa cewa ya fi abokin zamansa
- Sa’ad III ya jaddada muhimmancin kula da maƙwabta ba tare da la'akari da addininsu ko kabilar da suka fito ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Musulmai da kiristoci su daina zagin juna.
Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa dole mabiya addinai su hakura da juna idan dai ana son a zauna lafiya a Najeriya.

Source: Getty Images
The Cable ta ce Sarkin Musulmi ya yi wannan magana ne a wajen taron kasa-da-kasa da kungiyar Izala suka shirya a garin Abuja.
Jama’atu Izalatil Bidiah wa Iqamatis Sunnah ta shirya wannan taro da hadin kan kungiyar Muslim World Legue ta Saudi Arabiya.

Kara karanta wannan
"Kiristanci na cikin matsala"; Malamin addini ya dauki zafi kan kalaman Sheikh Jingir
Sarkin Musulmi ya fadi hanyar samun zaman lafiya
Sultan ya ce dole a fada wa kai gaskiya, Kiristoci sun daina zagin Musulmai, haka su ma sun daina zagin Kiristoci za a zauna lafiya.
Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Musulmai da Kiristoci bai kamata su rika jin sun fi wani ba, ya ce kowa daidai yake wajen Ubangiji.
Ya ce ba su zo taron domin fadin cewa sun fi wani ba, yake cewa Ubangiji ne ya halacci kowa kuma shi ne zai zabi wanda ya fi wani.
A lokacin da ake ta surutu game da kalaman Sani Jingir, Sarkin Musulmi ya nuna cewa babu wanda zai yi tunkahon ya fi danuwansa.
Sarkin Musulmi bai kama sunan Sheikh Sani Jingir ba, amma ana ganin jawabin ya zo a daidai.
Jaridar Leadership ta ce sarakuna, jami’an gwamnati da manyan malamai sun halarci wannan gagarumin taro da aka yi a birnin tarayya.

Source: Getty Images
'A guji yada kiyayyar juna' - Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji kawo kiyayya ta hanyar nuna bambancin kabilanci ko kuwa addini.
Ya nemi a dawo dawo da tarbiyyar da aka sa mutanen Najeeriya da shi na kula da makwabci ba tare da la’akari da yare ko addini ba.
A nan ya tuna wa kowa da labarin marigayi Abubakar Abdullahi, limamin da ya boye kiristoci fiye da 200 lokacin da ake rikici a Filato.
Basaraken ya nuna takaici game da yadda ake cin mutuncin juna a shafukan sada zumunta, ya ce ta kai ana yi wa shugabanni sharri.
Ga duk wadanda suka kirkiri karya suka jingina wa shugaban kasa, gwamnoni ko sanatoci, Sultan ya ce za su hadu da Ubangijinsu.
Sarkin Musulmi ya yi umarni da addu'o'i
Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci Musulmai su yi ta addu’o’i
An ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmin ya ce yanayin rashin tsaron a ƙasar na ƙara tabarbarewa saboda ayyukan 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane.
Sultan ya yi kira ga al'umma da su kasance masu tsoron Allah, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jama'a da jami'an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar.
Asali: Legit.ng
