Tarihin yadda Alex Ekwueme ya zama Mataimakin Shehu Shagari a 1978

Tarihin yadda Alex Ekwueme ya zama Mataimakin Shehu Shagari a 1978

Jaridar The Cable ta yi wani waiwaye inda ta kawo tarihin yadda Alex Ekwueme ya zama Mataimakin Shugaba Shehu Shagari a mulkin jamhuriya ta biyu. Mun tsakuro yadda abin ya wakana:

Tarihi ya nuna cewa a karshen shekarar 1978 ne manyan ‘Yan siyasa irin su su Aminu Kano, Samuel Gomsu Ikoku, Abubakar Rimi, Sule Lamido, Balarabe Musa, Dr. Junaid Muhammed, da Sabo Barkin Zuwo ka kafa Jam’iyyar NPN wanda ta karbi mulki a shekarar 1979.

Tarihin yadda Alex Ekwume ya zama Mataimakin Shehu Shagari a 1978
Ekwueme ya zama Mataimakin Shugaban kasa a 1979

Daga baya dai wadannan ‘Yan siyasa duk sun bar NPN su ka koma Jam’iyyar PRP da Malam Aminu Kano ya kafa. Marigayi Aliyu Makaman Bida wanda yana cikin manyan kasar tun bayan 'yanci su ka rike Jam’iyyar NPN wanda tana cikin Jam’iyyun da su ka shiga takarar zaben 1979.

KU KARANTA: APC ta amince cewa akwai matsala a tsarin Najeriya

A Oktoban 1978, Jam’iyyar NPN ta zauna, inda ta shirya fito da ‘dan takarar Shugaban kasa daga Arewa sannan kuma Mataimakin sa daga Kasar Ibo da sauran kujeru. A karshen 1978 aka yi zaben fitar da gwani inda Shehu Shagari yayi nasara biye da su akwai Dan Masanin Kano da Adamu Ciroma.

Sauran wadanda su kayi takarar sun hada da Olusola Saraki da JS Tarka da Iya Abubakar. Bayan Shehu Shagari ya lashe zaben ne sai ya dauko Alex Ekwume kamar yadda aka yi yarjejeniya a matsayin Mataimakin sa. Haka kuma aka yi su ka lashe zaben ya su ka hau mulki a 1979.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng