Tsohon Minista Ya Hasko Barnar da Sheikh Jingir Zai Yi wa Tinubu a Zaben 2027
- Femi Fani-Kayode ya buƙaci Sheikh Yahaya Jingir da ya daina amfani da addini wajen neman goyon bayan siyasa
- Ya bayyana cewa APC tana bukatar Musulmai da Kiristoci su goyi bayan takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima
- FFK bai ji dadin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rika murna da abin da Sheikh Jingir ya fada wajen auren gata a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Femi Fani-Kayode wanda yake shirin zama Jakadan Najeriya a kasar waje ya soki kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Sheikh Sani Yahaya Jingir wanda shugaba ne a kungiyar Izala ya yi maganganun da suka fusata musamman kiristoci a kasar nan.

Source: Facebook
Femi Fani-Kayode ya soki Sheikh Sani Jingir
Cif Femi Fani-Kayode ya yi rubutu a dandalin Facebook yana mai cewa kalaman malamin Musuluncin za su iya kawo sabanin addini.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Sheikh Jingir ya yi ƙarin bayani kan kalamansa da suka tayar da ƙura a Najeriya
Baya ga yiwuwar samun rikici, tsohon ministan tarayyan ya ce kalaman Sheikh Yahaya Jingir na iya jawo a kebe Kiristoci wajen zabe.
Wani abin damuwa da ya hango shi ne jam’iyyun adawa su yi amfani da wannan wajen kawo wa APC matsala a zabe mai zuwa.
Bayan jin abin da Jingir ya fada wa wajen auren gata a Kano, Fani-Kayode ya ce Musulmai da Kiristoci fiye da 100 sun tuntube shi.
FFK bai ji dadin aikin Abba Kabir ba
Bai tsaya a kan Jingir ba, a rubutun da ya yi, ‘dan siyasar ya nuna takaicinsa da yadda ya ga Gwamnan Kano yana murna da matsayar shehin.
"Abu daya ne ya fi wannan muni kuma shi ya bata mani rai fiye da abin da ya fada kuma shi ne ganin aboki kuma ‘danuwa na, Gwamnan Kano, yana jinjina masa kuma yana murna da haka."
- FFK
Jakadan na kasar Afrika ta Kudu mai jiran kama aiki ya gargadi ‘yan siyasa da su guji da amfani da addini wajen samun goyon bayan jama’a.
Yin hakan a cewarsa yana da tasiri har bayan zabe kuma zai iya kara jawo abubuwa su cabe.
Halin da Jingir zai iya jefa APC
'Dan siyasar ya kara da aika gargadi:
"Ba za mu yi shiru muna kallo ana bata addininmu ba saboda siyasa ba. Lamuran addini da ceto sun fi komai da za mu gani ko mu samu a duniyar nan muhimmanci."
Rubutun ya soki kalaman Jingir a kasa da ake da miliyoyin kiristoci musamman da ake zargin gwamnatin Najeriya da rashin yi masu adalci.
FFK kamar yadda aka fi saninsa da shi, ya ce a karshe kalaman za su iya raunana APC a zabe domin shehin yana jefa ‘yan takaransu a matsala.
"Siyasa da harkokin mulkin duniya za su kare amma addini wani sha’ani ne na har abada. Dole a daina wadannan maganganu na rabuwar kai kuma mu daina tsokano tsuliyar dodo.
“Abin da ya yi yana ba ‘yan adawa damar samun abin da za su yake mu da shi kuma wannan abin takaici ne.
"Muna bukatar kuri’un duka Musulmai da Kiristoci kafin mu iya cin zabe."
- Femi Fani-Kayode
Ahmad Gumi ya ba Sheikh Jingir uzuri
Wajen yi wa Sheikh Sani Jingir, ana da labari Dr. Ahmad Gumi ya yi magana, bulaliyarsa ta shaude ‘yan adawa da Peter Obi.
Dr. Ahmad Gumi bai kyale kowa ba wajen martani kan kalaman Sheikh Jingir, amma duk da haka ya yi wa shugaban na Izala uzuri.
Malamin yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen goyon bayan Bola Tinubu saboda ya dauki Musulmi a matsayin mataimakinsa tun 2023.
Asali: Legit.ng

