Kofa Ta Bude: Jerin Kasashe 2 da 'Yan Najeriya Za Su Iya Shiga ba Tare da Biza ba

Kofa Ta Bude: Jerin Kasashe 2 da 'Yan Najeriya Za Su Iya Shiga ba Tare da Biza ba

  • ’Yan Najeriya za su iya shiga Chadi da Jamhuriyar Congo ba tare da neman biza tun kafin tafiya ba daga ranar 1 ga watan Janairu, 2027
  • Kasashen biyu sun ce matakin zai sauƙaƙa zirga-zirga da kasuwanci tsakanin ƙasashen nahiyar Afirka
  • Sauyin na cikin ƙoƙari da matakan da kasashe je dauka don ƙarfafa haɗin kan Afirka da zirga-zirgar jama’a cikin nahiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nigeria - Masu riƙe da fasfon Najeriya za su samu damar shiga ƙasashen Afirka biyu ba tare da neman biza tun kafin tafiya ba daga ranar 1 ga Janairu, 2027.

Gwamnatocin Chadi da Jamhuriyar Congo, wadda aka fi sani da Congo-Brazzaville, sun sanar da shirin cire sharuddan biza ga ‘yan ƙasa daga dukkan ƙasashen Afirka.

Jirgin sama.
Jirgin sama yana tsakiyar tafiya da hoton fasfon Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Vanguard ya nuna cewa matakin zai bai wa ’yan Najeriya damar ziyartar ƙasashen biyu ba tare da samun bizar shiga ƙasar kafin tafiya ba, duk da cewa za a iya buƙatar wasu ƙananan matakai na tsaro.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya tona yadda yan siyasa ke gwara yan Najeriya da sunan addini

Shirin na cikin ƙoƙarin da ake yi a nahiyar Afirka na sauƙaƙa zirga-zirgar mutane, bunƙasa kasuwanci da ƙarfafa haɗin kan ƙasashen nahiyar.

Chadi za ta cire biza ga yan Najeriya

Gwamnatin kasar Chadi za ta soke sharadin biza ga ’yan ƙasa daga ƙasashen Afirka daga 1 ga Janairu, 2027.

Shugaban ƙasar, Mahamat Idriss Déby Itno, ya sanar da manufar a watan Yulin 2026, yana mai cewa matakin na da nufin ƙarfafa haɗin kan Afirka da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki a nahiyar.

A ƙarƙashin sabon tsarin, ’yan Najeriya da sauran ’yan ƙasashen Afirka za su iya shiga Chad ba tare da neman bizar shiga ƙasar tun kafin tafiya ba.

Wannan na iya sauƙaƙa tafiye-tafiye tsakanin Najeriya da Chadi, musamman ga masu kasuwanci da sauran matafiya.

Congo za ta bi sahun Chadi

Jamhuriyar Congo ma za ta cire sharadin biza ga dukkan ’yan ƙasashen Afirka daga 1 ga Janairu, 2027.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan Najeriya za su nemi tallafin ECOWAS na dala 65,000

Shugaban ƙasar, Denis Sassou Nguesso, ya sanar da matakin ne yayin taron shekara-shekara na Bankin Raya Afirka na 2026 da aka gudanar a Brazzaville.

Ya ce daga farkon shekarar 2027, ’yan ƙasa daga dukkan ƙasashen Afirka ba za su buƙaci biza domin shiga Jamhuriyar Congo ba, sai dai wasu ƙananan buƙatun gudanarwa da na tsaro.

Gwamnatin ta ce manufar za ta taimaka wajen ƙara haɗin kan ƙasashen Afirka da sauƙaƙa zirga-zirgar ’yan Afirka a nahiyar.

Haka kuma, matakin na iya taimakawa wajen cimma manufofin African Continental Free Trade Area (AfCFTA), wanda ke da burin ƙara habaka kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka.

An hana yan kasashe 3 shiga Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumomin Saudiyya sun dakatar da shigar matafiya daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Uganda da Sudan ta Kudu.

An kuma dakatar da bayar da kowane irin bizar shigaBSaudiyya ga mutanen da suka zauna a ɗaya daga cikin waɗannanBƙasashe cikin kwanaki 21 kafin tafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262