NUPRC: Ana Yi wa Masu Neman Aiki a Hukumar Man Fetur Ungulu da Kan Zabo
- Hukumar NUPRC ta ce yanzu haka akwai masu damfarar matasan da ke neman aiki da sunanta ana mika masu takardun bogi
- An gano cewa wadannan fitinannun 'yan damfara na karbar kudi daga jama'a da sunan taimaka musu samun aikin yi a hukumar NUPRC
- Hukumar ta ja kunnen jama'a musamman ganin cewa ana raba su da dukiyarsu a kan aikin da babu shi, tare da bayyana matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja– Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ta gargadi jama'a kan yawaitar takardun daukar aiki na bogi da ake kirkira.
Ta ce ana samar hanyar amfani da fasahar basirar na'ura mai kwakwalwa (AI), wadanda ake sanyawa sunayen mutanen da ba su da alaka da hukumar.

Source: Getty Images
The Cable ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Eniola Akinkuotu, ya fitar ranar Talata 11 ga watan Agusta, 2026, NUPRC ta ce ta samu rahotannin wasu bata-gari da ke karban kudi da sunan samar wa jama'a aiki.
NUPRC: 'Babu a daukar ma'aikata'
Jaridar Vanguad ta wallafa cewa hukumar ta bayyana cewa ta kai rahoton ayyukan wadannan masu damfara ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.
Sanarwar ta ce:
“Yayin da NUPRC ta kai rahoton ayyukan wadannan masu aikata laifuka ga hukumomin tsaro kuma take jiran sakamakon bincike, ana shawartar jama'a su yi taka-tsantsan domin kada su fada tarkonsu."
Hukumar ta ce idan ta yanke shawarar fara daukar ma'aikata a nan gaba, za a gudanar da tsarin ne bisa dokokin da ake da su da kuma ka'idojin gwamnatin tarayya.
Ana raba takardun aiki na bogi
A watan Fabrairu, Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta NMDPRA ita ma ta yi irin wannan gargadin, inda ta bayyana cewa ba ta gudanar da wani shirin daukar ma'aikata a kowane mataki.

Source: Facebook
NMDPRA ta ce akwai yiyuwar wasu kungiyoyin damfara na bogi ne ke shirya irin wadannan dabaru domin yaudarar masu neman aiki da karbar kudinsu.
Hukumar ta bukaci jama'a da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani kan daukar aiki kafin su bayar da kudi ko bayanan sirri ga kowa.
Tinubu ya amince a dauki aiki
A baya, kun samu labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da fara ɗaukar malamai 3,252 na ƙungiyoyin iyaye da malamai (PTA) aiki a gwamnatin tarayya bayan tantance su da tabbatar da cewa sun cancanta.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce matakin zai rage ƙarancin malamai a Kwalejojin Haɗin Kai da na Fasaha tare da inganta ilimi, inda ya bayyana wadanda za su iya shiga shirin domin su zama cikakkun malamai.
A cewar ministan, za a ba da fifiko ga malaman PTA da aka tantance, musamman waɗanda suka shafe shekaru da dama suna koyarwa a Kwalejojin Haɗin Kai da Kwalejojin Fasaha wanda ba su zama ma'aikata ba.
Asali: Legit.ng

