Kungiyar Dattawan Arewa Ta Yi wa Tinubu, Kwankwaso, Atiku, Obi Kudin Goro kan Zaben 2027

Kungiyar Dattawan Arewa Ta Yi wa Tinubu, Kwankwaso, Atiku, Obi Kudin Goro kan Zaben 2027

  • Kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF, ta bayyana damuwa game da salon mulkin Bola Tinubu bayan zaɓen 2023
  • Ya ce Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su gabatar da sahihin tsarin da zai gamsar da Arewa ba
  • Kungiyar ta bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da talauci za su yi tasiri a zaɓen 2027 da ake tunkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Farfesa Tukur Mohammed-Baba, ya yi magana game da zaben 2027.

Mohammed-Baba ya ce Shugaba Bola Tinubu ya rasa wani bangare da matsayi na siyasa a Arewa tun daga shekarar 2023.

Kungiyar ACF ta dura kan Tinubu, Kwankwaso, Obi game da zaben 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Mohammed-Baba ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin PrimeTime na Arise TV, inda ya soki tsarin siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

'Haka aka yi wa Jonathan': Malami ya hango makarkashiya ga Tinubu a 2027

ACF ta caccaki salon yan siyasar Najeriya

A cewarsa, 'yan siyasar ƙasar ba su da ingantattun manufofi, kuma galibinsu suna tafiyar da siyasa ne bisa muradun kansu.

Ya ce dukkan jam'iyyun siyasa sun gaza magance matsalolin rashin tsaro da kuma ƙalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta.

Ya ce:

"Ban ga wata jam'iyya da ta fito da cikakkiyar manufa ko akidar siyasa ba. Talakan ɗan Arewa ya daɗe yana jin takaici."

Ya ce an gwada dukkan nau'ikan lissafin siyasa kamar ɗan takarar Arewa da tikitin Musulmi da Musulmi amma ba su kawo mafita ba.

Game da Tinubu, Mohammed-Baba ya ce manufofin tattalin arzikinsa sun haifar da takaici da damuwa ga rayuwar al'umma.

Ya ƙara da cewa duk da bayanan gwamnati, matsalar rashin tsaro tana ci gaba da taɓarɓarewa a sassan ƙasar.

Ya ce an fara kure al'umma da tsarin ceton kai saboda mutane sun fara ganin gwamnati ba za ta kare su ba.

Da yake magana kan Atiku Abubakar, ya bayyana shi a matsayin ɗan takara mai nacin neman mulki ba tare da sabon tsari ba.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

"Ban ga abin da ya gabatar a matsayin mafita ba face cewa wannan gwamnati ta gaza. Ina hujjar?"

- In ji Mohammed-Baba

ACF ta caccaki Peter Obi da Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

ACF ta juyo kan takarar Obi da Kwankwaso

Game da Peter Obi, ya ce ya rasa wasu masu goyon baya a Arewa saboda yawaitar sauya jam'iyyu.

Ya ce mutane na tambayar ainihin abin da Obi yake nema, kasancewar ya yi anfani da jam'iyyu daban-daban.

Mohammed-Baba ya kuma soki wasu kalaman Rabiu Kwankwaso, yana cewa suna ci wa tarihin Arewa mutunci.

Ya ce babu wani daga cikin waɗannan 'yan siyasa da ya gabatar da takamaiman mafita kan tattalin arziki, tsaro ko ababen more rayuwa.

Babachir ya soki Tinubu, Atiku da Kwankwaso

A baya, an ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya caccaki APC, PDP, ADC da NDC, yana cewa dukkan manyan jam’iyyun ba su ba da manufa.

Babachir ya ce zai iya zaɓar matashin ɗan takara a 2027, amma ya bayyana rashin gamsuwa da dukkan manyan ‘yan takarar da ake da su yanzu a Najeriya.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya wanda Muhammadu Buhari ya kora daga ofis ya ce ya yi murabus daga ADC saboda zargin rashin gaskiya a zaben fitar da gwani da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.