Jerin Jihohin da APC za Ta Yi Zaben Fitar da Gwani bayan Gaza Yin Sasanci

Jerin Jihohin da APC za Ta Yi Zaben Fitar da Gwani bayan Gaza Yin Sasanci

Gombe, Nasarawa da wasu jihohin Najeriya za su yi zaben fitar da gwani bayan wasu masu neman takara sun ki amincewa da yarjejeniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026 jam'iyyar APC ta tsara cewa za ta gudanar da zaben fitar da gwani na gwamna.

Jihohin da suka gaza cimma matsaya kan fitar da 'yan takara ta hanyar sulhu za su fafata a zaben fitar da gwani kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Shugaban APC, Nentawe Yilwatda
Shugaban APC na bayani a wajen taro a Abuja. Hoto: Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku jihohin da suka gaza cimma yarjeneniya wanda hakan ya tilasta jam'iyyar shirya zaben 'yar tike.

1. Za a yi 'yar tike a Gombe

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya sanar da cewa jam'iyyar APC za ta shirya zaben fitar da gwani bayan korafe-korafe.

Kara karanta wannan

Bayan Pantami, malamin Musulunci, Sheikh Bashir ya rasa takarar gwamna a Sokoto

Hakan na zuwa ne bayan Sheikh Isa Ali Pantami da Sanata Saidu Ahmed Alkali sun ki amincewa da fitar da Jamilu Isiyaku Gwamna da jam'iyyar ta yi.

Gwamna Inuwa Yahaya da Jamilu Gwamna
Shugaban APC ya daga hannun Jamilu Gwamna a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

A wani sako da mai magana da yawun gwaman Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya fitar a Facebook, ya ce jami'an tsaro sun shirya domin tabbatar da zaben ya gudana lami lafiya.

2. Yobe za ta yi zaben fitar gwani

Gwamna Mala Buni na jihar Yobe State ya ce jam’iyyar APC ta himmatu wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani cikin ’yanci, adalci da gaskiya idan aka gaza cimma matsaya.

Rahotanni sun nuna cewa masu neman takarar gwamna shida na APC a jihar sun yi watsi da ɗan takarar da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka amince da shi, Baba Wali, tare da neman a yi zabe.

Baba Malam Wali da gwamna Mai Mala Buni
Shugabannin APC a Yobe sun daga hannun wanda suke so ya yi takara. Hoto: Mamman Mohammed
Source: Facebook

Masu neman takarar sun haɗa da Ibrahim Bomoi, Bashir Machina, Kashim Musa-Tumsah, Mustapha Maihaja da Lawan Kolo.

Rahoton Punch ya nuna cewa Sanata Ahmad Lawan da tsohon sufeto janar na ’yan sanda, Mohammed Baba sun janye da batun takara a jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aika sako ga 'yan APC ana shirin fara zaben fitar da gwani

3. Jihar Nasarawa ta bi sahu

Wasu masu neman takara a jam'iyyar APC a jihar Nasarawa sun yi watsi da dan takarar da gwamna Abdullah Sule ya amince da shi.

Tsohon sufeto janar na ’yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya tabbatar wa al’ummar ƙaramar hukumar Karu cewa yana da ƙarfin da zai iya kayar da ɗan takarar da gwamna Abdullahi Sule ke marawa baya, Sanata Aliyu Ahmed Wadada.

The Guardian ta wallafa cewa Mohammed Adamu ya ce yana da tabbacin zai yi nasara idan aka gudanar da zaɓen fitar da gwani cikin gaskiya da adalci.

Gwamna Abdullahi Sule, Bola Tinubu da Ahmed Wadada
Shugaba Bola Tinubu a tsakiyar gwamna Abdullahi Sule da Ahmed Wadada. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

4. APC za ta yi zabe a Oyo

Shugabannin jam'iyyar APC a jihar Oyo sun amince da Sharafadeen Alli a matsayin wanda zai yi mata takara a 2027, lamarin da ya samu kin amincewa daga tsohon ministan makamashi, Bayo Adelabu.

Vanguard ta wallafa cewa kin amincewar tsohon ministan ya kai ga jam'iyyar daukar matakin gudanar da zaben fitar da gwani a mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

NDC: Jam'iyyar su Kwankwaso ta fitar da kudin fom din takarar 2027

Adebayo Adelabu a wajen taron siyasa
Adebayo Adelabu na bayani a taron APC a Oyo. Hoto: Bayo Adelabu
Source: Facebook

Mai neman takarar gwamna, Sharafadeen Alli ya bayyana shirinsa na shiga zaɓen fitar gwani na jam’iyyar APC kamar yadda wasu masu neman takara ke nema.

5. Ba a sasanta a Taraba ba

An yi tsammanin sauya sheƙar gwamnan Taraba Agbu Kefas daga jam’iyyar PDP zuwa APC zai share masa hanyar neman wa’adi na biyu ba tare da tangarda ba

Sai dai alamu sun nuna zai fuskanci zaɓen fitar da gwani a cikin jam’iyya mai mulki, sabanin wasu gwamnoni masu ci a wasu jihohi da suka samu amincewa a matsayin ‘yan takara su kaɗai.

David Sabo Kente
David Sabo Kente da ke neman takara a Taraba. Hoto: Abdulmumin Imam
Source: Facebook

Jaridar nan ta The Nation ta rahoto shugaban APC na Taraba yana cewa duk mai neman tikitin gwamna a jam'iyyarsu, kofa a bude ta ke gare shi ya fito a gwabza.

Tuni daya daga cikin masu neman takara, David Sabo Kente ya ce ba zai janye ba, zai shiga zaben tsaida gwani.

Kara karanta wannan

'Yadda 'yan Arewa za su zabi Tinubu a 2027,' Uba Sani ya fito da bayanai

An taru a hedikwatar jam'iyyar APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa masu neman takara sun cika sakatariyar jam'iyyar APC domin sanin sakamakon tantance su da aka yi.

Wani rahoto ya nuna cewa dole sai an yarda mutum ya tsallake tantancewa kafin ya samu damar shiga zaben fitar da gwani da za a fara a makon nan.

Wasu bayanai da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa daga sakatariyar APC, masu neman takarar sun wuce gidan shugaban jam'iyyar a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng