Daliban Borno da aka Sace Sun Doshi Kwana 100 a Hannun 'Yan Ta'adda
- Kwana 87 bayan tsagerun 'yan bindiga sun sace ɗaliban makarantar firamare da sakandare ta Mussa a ƙaramar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno, iyayen yaran sun yi korafi
- Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, 15 ga Mayu, 2026, wato da misalin karfe 9:00 na safe lokacin da maharan suka mamaye makarantar tare da sace yaran
- Iyayen yaran sun nuna matukar yanke ƙauna a yayin da suke magana da 'yan jarida, inda suka bayyana cewa har yanzu ba su samu wani labari a hukumance daga wurin gwamnatoci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Maiduguri – Iyayen ɗaliban da aka sace daga makarantar firamare da ta sakandare ta Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba a jihar Borno sun yi hira da manema labarai.
Sun bayyana cewa suna cikin baƙin ciki, kuma firgicin da suke ciki na karuwa kullum, kwanaki 87 bayan sace 'ya'yan nasu.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa wani uba, Sale Buba, ya bayyana cewa tun bayan da aka yi gaba da yaran babu wani tsagera ko ƙungiya da ta fito ta amsa alhakin sace su ko neman kuɗin fansa.
Ya bayyana cewa:
"Kimanin watanni uku yanzu, halin da muke ciki na rashin tabbaci na ci gaba da haɗdasa mana firgici.
"Muna rayuwa cikin tsoro da rashin tabbas a ko da yaushe. Mata gaba ɗaya kuka suke yi kullum, su kan rasa barci saboda tunanin halin da yaran suke ciki a hannun 'yan bindiga, musamman a wannan lokaci na ruwan sama."
Korafe-korafen iyayen daliban
Shugaban kungiyar iyayen yaran da aka sace, Ishaya Suya, ya soki shirun da hukumomin jiha da na tarayya suka yi kan lamarin, inda ya kwatanta shi da wani nau'i na azabtarwa ga iyayen.
Ya ce ko a jihar Oyo, an sace yara a ranar guda amma gwamnan jihar ya yi duk mai yiwuwa aka ceto su har aka yanke wa ma'aikatan aikin hukunci, yayin da a bangarensu ake kukan neman dauki amma shiru ake ji.
Gwamnati da 'yan majalisun yankin, ta bakin kansila Peter Haruna Waba, sun bukaci iyayen da su kwantar da hankulansu yayin da gwamnati ke yin duk mai yiwuwa don ganin yaran sun koma gida lafiya.

Source: Original
Haka zalika, Ƙungiyoyin Fararen Hula (CSOs) a jihar Borno ta bakin shugabanta Abubakar Suleiman, sun yi Allah wadai da shirun da gwamnati ta yi, inda suka buƙaci a hanzarta gudanar da aikin ceto yaran ba tare da ɓata lokaci ba.
Me ya hana ceto yaran?
A gefe guda, wani jami'in tsaro da ya halarci taron ceto yaran da farko ya bayyana cewa ƙalubalen da suka fuskanta a cikin daji shi ne ya haifar da jinkirin aikin ceto yaran.
Trust Radio ya wallafa cewa jami'in ya bayyana cewa:
"Mun shiga cikin dajin da nufin ceto yaran inda muka ci karo da wani masallaci da ake tunanin an yi wofi da shi, inda muka tarar da wayoyin hannu fiye da 30 ana cajinsu da injin janareta.
"Sai dai ashe hakan wata makarkashiya ce da 'yan bindigar suka gitta mana. Bayan mun karɓe wayoyin, sun yi mana kwantan ɓauna mai tsanani."
A cewarsa, wannan kwantan ɓaunar ta kusa fin ƙarfin dakarun tsaro inda 'yan bindigar suka ƙwace motocin sojoji guda biyu da babura bakwai, lamarin da ya tilasta wa jami'an tsaron yin ja da baya da kuma maida hankali kan wasu dabarun tunkarar dajin.
'Yan bindiga sun sa haraji
A wani labarin daban, kun ji cewa wani manomi a ƙaramar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue ya tsere daga gonarsa bayan da tsagerun 'yan bindiga suka nemi biyan kuɗin fansa har N500,000 kafin su ba shi damar girbe amfanin gonarsa.
Ɗan manomin ya bayyana cewa mahaifinsa ya riga ya biya N200,000 ga 'yan bindigar amma duk da haka suna ci gaba da yi masa barazana don ya cika sauran N300,000 din.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron bita da SERAP ta shirya a garin Makurdi, inda ya ƙara da cewa 'yan bindigar sun kai wa gidansu hari tare da sace mahaifiyarsa.
Asali: Legit.ng


