'Ba Sulhu a Nasarawa' Tsohon IGP Ya Rusa Shirin APC, Ya Turje kan Takarar Gwamna
- Tsohon IGP, Mohammed Adamu, ya nuna rashin amincewarsa da tsarin maslaha wajen zaɓen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Nasarawa
- Adamu, wanda yana ɗaya daga cikin manyan masu neman tikitin takarar, ya ce tsarin zaɓen fidda gwani na kato-bayan-kato ne kawai za a amince da shi
- Wannan martani ya fito ne ta bakin Daraktan tuntuɓa na kungiyar yakin neman zabensa, Hon. Isah Nathaniel, a ranar Asabar a garin Lafia
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Nasarawa – Rikicin neman tikitin takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a jihar Nasarawa ya ɗauki sabon salo, bayan tsohon IGP Mohammed Adamu ya sayi fom din takara.
Mohammed Adamu, tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya fito fili ya ƙalubalanci duk wani yunƙuri na sanya tsarin maslaha a fitar da d'an takarar APC a Nasarawa.

Source: Facebook
Tsohon IGP ya rusa shirin APC a Nasarawa
Tsoho shugaban 'yan sandan, ya nuna cewa dukkan masu ruwa da tsaki na APC sun riga sun amince da yin zaɓen fitar gwani na kai-tsaye tun a wani taro da aka yi a gidan gwamnatin jiha da ke Abuja, in ji rahoton Leadership.
Adamu, wanda ya na daya daga cikin manyan masu neman tikitin takarar gwamnan a APC ya ce ba za su amince da duk wata hanyar fitar da dan takara da ta wuce da zaben kato bayan kato ba.
Ya yi wannan maganar ne ta bakin daraktan tuntuba da hado kan jama'a na kungiyar yakin neman zabensa, Hon. Isah Nathaniel a ranar Asabar.
A cewar Hon. Nathaniel, wannan mataki ya yi daidai da ra’ayin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganin kowane mamba na jam’iyya ya samu damar zaɓar wanda yake so.
Ya ƙara da cewa Gwamna Abdullahi Sule da kansa ya ba da tabbacin cewa tsarin zai kasance a buɗe kuma zai bi dokokin jam’iyyar da na zaɓe.

Kara karanta wannan
Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027
Rikicin "dan takara na musamman"
Nathaniel ya bayyana mamakin sa kan yadda aka fara maganar samun "ɗan takara na musamman" bayan ƴan kwanaki da kammala taron Abuja.
Ya jaddada cewa, gwamna yana da damar goyon bayan duk wanda yake so, amma hakan ba zai soke matsayar masu ruwa da tsaki ba.

Source: Facebook
Sannan ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na neman sulhu ko maslaha a wannan lokaci ya makara kuma ba za a amince da shi ba.
Hakazalika, ya ce suna adawa da duk wani nau’i na danniya ko yanke shawara daga mutum guda ba tare da bin ƙa’ida ba.
Tsohon IGP ɗin ya tabbatar da cewa ya riga ya sayi fom ɗin tsayawa takara da na nuna sha’awa kamar yadda doka ta tanada.
Nasarawa: Tsohon IGP ya sayi fom a APC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon IGP, Mohammed Adamu, ya ƙi amincewa da tsarin maslaha wajen zaben d'an takarar gwamna a Nasarawa.

Kara karanta wannan
Mai son takarar gwamna a APC ya ki yarda da zabin Tinubu, ya yi barazanar zuwa kotu
Adamu, ya sayi fom din neman tsaya wa takara a karkashin jam'iyyar APC, lamarin da ya saba da matsayar Gwamna Abdullahi na nuna magajinsa.
Ofishin yakin neman zaben Adamu, ya ce tsohon IGP yana da farin jini, zai iya lashe tikitin takara a zaben fitar da gwani kuma ya ci zaben gwamna.
Asali: Legit.ng
