Bayan Pantami, Malamin Musulunci, Sheikh Bashir Ya Rasa Takarar Gwamna a Sokoto

Bayan Pantami, Malamin Musulunci, Sheikh Bashir Ya Rasa Takarar Gwamna a Sokoto

  • Malamin addinin Musulunci, Sheikh Bashir Sani Ahmad Sokoto ya sanar da cewa bai samu tikitin takarar gwamna ba a jam'iyyar ADC
  • Ya bayyana haka ne yayin da jam'iyyun siyasa ke kokarin fitar da 'yan takara a hanyar sulhu ko kuma zaben fitar da gwani a Najeriya
  • A watan Ramadan da ya gabata ne babban malamin ya ayyana cewa zai tsaya takarar gwamnan Sokoto domin ceto jihar kuma ya kawo cigaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Sheikh Bashir Sani Ahmad Sokoto ya sanar da magoya bayan shi cewa jam'iyyar ADC ba ta tsayar da shi a matsayin dan takarar gwamna ba.

Hakan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta ki zaben daya daga cikin malaman Musulunci da suka nemi takara a Gombe, wato Sheikh Isa Ali Pantami.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya manta da PDP, zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar hadaka

Sheikh Bashir Sani Ahmed Sokoto
Lokacin da Sheikh Bashir A, Sani ke wa'azi a Sokoto. Hoto: Sheikh Bashir Sani Ahmed Sokoto
Source: Facebook

Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya sanar da cewa bai samu damar takara ba ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sheikh Bashir Sokoto bai samu takara ba

Da asubahin ranar Juma'a, 15 ga watan Mayun 2026 Sheikh Bashir Sani Sokoto ya sanar da cewa ba shi jam'iyyar ADC ta tsayar takara ba.

A sakon da ya wallafa, Sheikh Bashir ya ce:

"Assalamu alaikum warahmatullah masoyanmu na birni da kauye,
"Kamar yadda ku ka sani mun fito muna neman takarar gwamnan jihar nan tamu mai albarka ta Sokoto domin mu fitar da talakawan jihar daga cikin mawuyacin halin da suke ciki,
"Cikin iyawar Allah jam'iyyar mu ta ADC ba ni ta tsayar a matsayin dan takara ba!!!"

Bayan sanarwar cewa ba shi aka tsayar ba, malamin ya kara da cewa:

"Alhamdulillahi, mun godewa Allah kuma muna kara yi masa godiya a kan karbuwa da kuma soyayyar da jama'a suke nuna mana cikin birni da kauye."

Kara karanta wannan

Jerin jihohin da APC za ta yi zaben fitar da gwani bayan gaza yin sasanci

Malamin ya bukaci masoya da magoya baya a duk inda suke su kwantar da hankalinsu kuma su rike soyayya da goyon bayan da suke nuna masa, kada su karaya ko jikin su yayi sanyi.

Wane ne jagoran ADC a Sokoto?

Malamin ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki sun yarda cewa shi ne jagoran tafiyar a jihar Sokoto duk da cewa bai samu takara ba.

Ya ce:

"Sun yarda ni ne jagoran tafiyar nan tamu insha Allahu da yardar Allah, Allah zai bamu nasara.
"Mun gode."
Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto da Aminu Waziri Tambuwal
Sheikh Bashir Sokoto da jigon ADC, Aminu Tambuwal. Hoto: Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto
Source: Facebook

Duk da cewa bai samu takara ba, malamin ba sanar da cewa ba zai fice daga jam'iyyar ba ko kuma ya nemi a yi zaben fitar da gwani.

'A yi zaben fitar da gwani' - Pantami

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami da ke neman takarar gwamna a Gombe ya ce a shirye ya ke a zaben fitar da gwani da APC za ta yi.

Malamin ya sanar da cewa yana da kwarewar da zai jagoranci jihar Gombe, kuma akwai muhimman abubuwa da suka bambanta shi da sauran masu son takara.

Sheikh Pantami ya nemi a yi zaben fitar da gwani ne bayan gwamnan Gombe ya fitar da dan takara amma ya ce bai amince da hanyar fitar da shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng