Yadda Albashin Sojoji 250, 000 Ya Canza sakamakon Karin da Tinubu Ya Yi

Yadda Albashin Sojoji 250, 000 Ya Canza sakamakon Karin da Tinubu Ya Yi

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsarin albashin sojojin Najeriya wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba 2026
  • Babu kurtun soja da za a rika biya kasa da N180, 000 domin kuwa an yi wa kowa karin kudin da ya kai 30% zuwa 80% a Najeriya
  • A ƙarƙashin sabon tsarin, albashin soja mai matsayin Private zai koma ₦187,200 yayin da Janar zai rika samun ₦3.25m a wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Sabon tsarin albashin sojoji da Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi zai faranta ran mafi yawan dakarun Najeriya.

A sanadiyyar karin kudin da Mai girma shugaban kasa ya yi, za a samu sojojin da ke tashi da sama da N3m a kowane wata.

Sojoji
Sojojin Najeriya a bakin aiki da kuma hoton jami'ai rike da kudi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sojoji 250, 000 sun samu karin albashi

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa karamin soja shi ne zai koma karbar N187, 2000 a duk wata bayan karin da aka yi.

Kara karanta wannan

Za a samu alheri: Manhajar X ta canza salo, ta kawo sabon tsarin da mutane za su samu kuɗi

Canjin da aka samu wanda ya kai 30% zuwa 80% zai jawo babban janar na soja kuwa zai rika karbar N3.25m a karshen wata.

Wannan sauyi da zai shafi jami’an sojoji har 250, 000 zai fara aiki ne daga watan Satumba a cewar Cif Bayo Onanuga.

Maimakon N660bn da ake kashewa albashin sojoji a Najeriya, Gwamnatin tarayya za ta rika batar da N924bn a duk shekara.

Sojan da yake matsayin Kanal zai samu karin 30% a albashinsa, haka abin yake ga janarori da Birgediya, Manjo da Laftanan.

Karin albashin da aka yi wa kananan sojoji

Kananan sojoji da ke bayan Kamal har zuwa kuratan da ke matsayin warrant officer za su ga karin albashin da ya kai 80%.

An gano karamin kurtu na Private mai karbar N104, 000 zai koma samun N187,200 a yanzu.

Shi ma lance corporal da ake biya N112,000 a wata zai samu karin N89, 600. Albashin shi zai tashi zuwa N201,600.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Kofur mai tashi da N115,000 a karshen wata zai koma karbar N207, 000 daga yanzu, an yi masa karin fiye da N90,000 a wata.

Albashin Sajen ya karu da N100,000, ya daina karbar N125,000 daga karshen Satumba.

Sannan warrant officer zai ga canji daga N170,000 da ake biyan shi zuwa N255,000, ma’ana dai an yi masa kari na N85,000.

Albashin master warrant zai dawo N315,000 sai kuma warrant officer zai ga karin albashi a duk watan duniya zuwa N345,000.

Sojojin Najeriya
Dakarun Sojojin Najeriya da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Karin kudin manyan jami'an sojoji

Wanda ya shiga aikin soja wato second lieutenant zai ga kari daga N240,000 zuwa N360,000, Laftanan zai rika samun N420,000.

Albashin Kyaftin zai koma N480, 000 maimakon N320, 000. Wanda yake Manjo a soja zai rika karbar albashin N570, 000 a wata.

Daga watan gobe, karin ya maida albashin Laftanan Kanal N630, 000 sai Kanal ya samu N870, 000.

Birgediya Janar zai ci karo da karin N225, 000 domin kudinsa zai koma N975,000, alhali N1.495m za su shiga aljihun Manjo Janar.

Laftanan janar zai ga kari daga N1.9m zuwa N2.47m kamar yadda cikakken Janar zai daina karbar N2.5m, zai rika samun N3.25m.

Kara karanta wannan

Bincike kan shirin yi wa Tinubu juyin mulki ya rutsa da fitaccen jarumin fim a Najeriya

Ma'aikata na neman sabon karin albashi

Ana da labari Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun buƙaci gwamnati ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata zuwa ₦500,000.

Mataimakin shugaban NLC na ƙasa, Audu Titus Amba, ya bayyana cewa wa'adin ƙarin ₦70,000 da aka amince a baya ya ƙare tun watan Yuli.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi alkawarin gabatar da sabuwar buƙatar ƙungiyoyin ƙwadagon a taron ƙungiyar gwamnonin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng