Bincike Ya Zo Ƙarshe, An Ji Dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki
- Jagoran wadanda ake zargi, Kanal Mohammed Ma’aji ya bayyana cewa shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ya samo asali tun 2023
- Ya ce rashin tsaro, cin hanci da rashawa da wasu manufofin tattalin arziki suna daga cikin dalilan da suka sa aka farfado da shirin juyin mulki
- An kama Ma’aji a watan Satumban 2025 yayin da ake gudanar da bincike kan zargin yunkurin juyin mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jagoran wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki, Kanal Mohammed Ma’aji na rundunar sojin Najeriya ya yi bayani kan dalilin kirkiro da wannan shiri.
Ya yi bayanin yadda shirin kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samo asali, kafin daga bisani jami’an tsaro su dakile shi a shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Dalilin da ya sa NRS ke ganin cire tallafin man fetur shi ne mafi alheri ga 'yan Najeriya

Source: Twitter
Rahotan Premium Times ya ce shirin ya kunshi wasu hafsoshin soji da suka hada da masu aiki da wadanda suka yi ritaya, da kuma wasu fararen hula da ake zargin an hada su cikin shirin.
An gano lamarin ne a karshen watan Satumban 2025, lamarin da ya kai ga kama mutane da dama da kuma gudanar da bincike a kansu.
Yadda aka fara shirin juyin mulki tun 2023
A cikin bayanin da Ma’aji ya bayar ga masu bincike na soji, ya ce tun a karshen mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ne aka fara tunanin shiga tsakani ta hanyar soji.
Ma’aji, wanda dan asalin jihar Neja ne dan dhekaru 50, ya ce rashin tsaro da ya addabi kasar ya kasance daya daga cikin abubuwan da suka sa wasu hafsoshin soji suka fara tunanin cewa ya kamata a dauki wani mataki.
A cewarsa, satar mutane da ‘yan bindiga sun mamaye sassan arewa, yayin da sojoji da fararen hula ke rasa rayukansu.

Kara karanta wannan
Lallai Tinubu ya sha da ƙyar, an gano manhajoji 2 da aka yi amfani da su a shirin juyin mulki
Ya ce wasu hafsoshin sun yi imanin cewa manyan jami’an soji za su dauki mataki domin shawo kan matsalar, amma hakan bai faru ba
“A lokacin ne tunanin juyin mulki ya ya fara,” in ji Ma’aji.
Ya kara da cewa wadanda suka shiga wannan yunkuri sun hada da hafsoshin da ke da irin wannan damuwa kan tabarbarewar tsaro da halin da kasar ke ciki.
An farfado da shirin a 2024
Ma’aji ya ce shirin ya sake daukar wani sabon salo a shekarar 2024 bayan da ya sake faduwa a jarabawar karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar.
Ya ce wannan shi ne karo na biyu da ya kasa samun karin girman, lamarin da ya sa wasu daga cikin mutanen da ke tare da shi suka matsa masa da ya farfado da abin da suka fara tun da farko.'.
Sun soki manufofin gwamnatin Tinubu
Ma’aji ya ce mutanen da ke cikin shirin juyin mulki sun yi imanin cewa halin da Najeriya ke ciki ya kara tabarbarewa a karkashin gwamnatin Tinubu idan aka kwatanta da zamanin Buhari.
Ya bayyana cire tallafin man fetur, sauya tsarin canjin kudin Naira, karin haraji da kudin wutar lantarki a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka jawo musu damuwa.
Ya kuma ambaci cin hanci da rashawa da rashin tsaro a matsayin manyan matsalolin da suke ganin gwamnati ta kasa shawo kansu.
Matasa da tsofaffin sojoji sun shiga damuwa
Kanal Ma’aji ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin matasan Najeriya suna cikin matsananciyar damuwa saboda rashin aikin yi, hanyar samun abin dogaro da kai da kuma rashin kyakkyawar fata ga makomarsu.

Source: Twitter
Ya kuma yi magana kan tsoffin sojoji da sauran wadanda suka yi ritaya daga ayyukan gwamnati, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun taba gudanar da zanga-zanga domin neman a biya su hakkokinsu, fansho da garatuti.
An kama Kanal Ma’aji a ranar 29 ga Satumban 2025, a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta soke bikin ranar samun ‘yancin kai na 1 ga Oktoba.
Manhajojin da suka yi amfani da su
Kun ji cewa masu bincike kan zargin yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun gano manhajojin da aka yi amfani da su.
Rahoto ya nuna cewa wasu da ake zargi da hannu a shirin juyin mulkin 2025 sun yi amfani da WhatsApp da Zangi wajen sadarwa.
Asali: Legit.ng
