Babu Zaman Lafiya a ADC, An 'Canza' ‘Dan Takarar ADC a Shafin Hukumar INEC
- Rikici ya barke a jam'iyyar ADC ta jihar Adamawa kan zargin sauya sunan dan takarar gwamna na zaben 2027
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya zargi shugabannin ADC da canza Umar Suleiman
- Kwamitin yakin neman zabe ya fito fili ya bugi kirji cewa ba a ba Modibbo Hamman Tukur Ribadu takara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Adamawa - Abubuwa sun canza a jihar Adamawa ga jam’iyyar ADC a sakamakon labarin da ake ji na canza ‘dan takarar gwamna a 2027.
Rade-radi suna yawa cewa ADC ta maye gurbin Suleman Umar wato Omarana da Modibbo Hamman Tukur Ribadu a shafin INEC.

Source: Getty Images
Rade-radin canza 'dan takarar gwamnan ADC
Da safiyar Litinin, Daily Trust ta rahoto cewa ana tunanin Modibbo Hamman Tukur Ribadu zai rike wa ADC tuta a jihar Adamawa.
Suleman Umar ya samu kan shi a matsala a jam’iyyar hamayyar ne a skamakon sauya shekar Babachir David Lawal a kwanakin baya.
Ana zargin cewa Babachir David Lawal ne ya dage sai da Omarana ya samu takara duk da mutanen Atiku suna da wanda suke so.
Da tsohon sakataren na gwamnatin tarayya ya sauya sheka kuma ya rika munanan maganganu, sai ake zargin an canza ‘dan takara.
A ranar 8 ga watan Agusta 2026 aka tsara za a daura sunayen ‘yan takara a zaben gwamnoni da majalisar dokoki a shafin hukumar INEC.
Daga baya INEC ta tsawaita wannan wa’adi zuwa ranar Talata 11 ga Agustan 2026.
Babachir David ya ce an canza 'dan takara
A wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Facebook, Babachir David Lawal ya fito yana cewa an canza Umar da wani yaron Atiku Abubakar.
A jiya yake cewa an hura wa shugabannin ADC wuta har sai da suka daura sunan Tukur Modibbo a matsayin ‘dan takara a shafin INEC.
INEC, Atiku da ADC ba su uffan ba
Da hukumar ta sanar da cewa an wallafa sunayen ‘yan takara na fadin jihohi, da aka duba ba a iya ganin sunayen masu takara a Adamawa ba.
Jaridar ta ce da aka tuntubi hedikwatar INEC a Abuja, sai ta ce ba a gama aikin ba tukuna.
An yi kokarin jin ta bakin ofishin Atiku Abubakar da Daniel Bwala wanda shi ne shugaban ADC na shiyyar Arewa maso gabas a karshen mako.
Sai dai ba a yi nasarar jin komai daga gare su ba, hakan ya bar jama’a cikin rudani.
Kwamitin takarar gwamnan Adamawa ya yi magana
Sanadiyyar haka, rikicin gida yana kara taba ADC a Adamawa wanda tun can an samu sabani har aka rasa wasu manyan ‘yan siyasa.
Shugaban kwamitin yakin neman zaben Omarana, Mark Wosi, ya fitar da jawabi yana cewa har yanzu takarar gwamna ta hannunsu.
Mark Wosi yana wannan magana sai aka ji Aminu Iyawa yana tabbatar da takarar tsohon shugaban NFIU, Hammar Tukur Ribadu a ADC.
Wata rigima a cikin jam'iyyar NDC
An ji labari reshe zai iya juye wa da mujiya a sakamakon zargin da aka yi wa Rabiu Musa Kwankwaso na neman murkushe kowa a NDC.
Shugaban NDC ya zargi Sanata Kwankwaso da shirya masa makarkashiya bayan karbar sa a jam’iyya da suka sauya-sheka daga cikin ADC.
An zargi tsohon gwamnan Kano da yin baba-kare, ya hana kowa takara a jam'iyyar sai mutanensa duk da cewa an yi alkawarin a raba mukamai.
Asali: Legit.ng


