Nasara daga Allah: Sojoji da Yan Sanda Sun Rutsa Yan Bindiga Fiyeda 200 Ta Sama da Ƙasa
- Dakarun sojojin Najeriya da ‘yan sanda sun yi artabu da yan bindiga fiye da 200 a kan iyakar jihohin Zamfara da Kebbi
- Rundunar ta hada sojojin Najeriya, Rundunar Sojin Sama da jami’an ‘yan sanda, kuma rahoto ya nuna an kashe yan bindiga da dama
- Har yanzu hukumomin tsaro ba su bayyana adadin wadanda suka mutu ko sakamakon farmakin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Sojojin Najeriya na kasa da na sama da ‘yan sanda sun yi wani kazamin artabu da 'yan bindiga 100 a yankin da ke tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
Majiyoyin tsaro sun ce ‘yan bindigar sun fito ne da dimbin yawa daga yankin Sangeko Gap da ke jihar Zamfara, inda suke kokarin kutss kai zuwa Makuku a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Source: Twitter
Vanguard ta ruwaito majiyoyin na cewa ‘yan bindigar sun rarrabu zuwa rukuni uku, inda ake zargin yawancinsu na tafiya ne a kan babura.
Jami'an tsaro sun yi artabu da yan bindiga
Wannan ci gaba ya kara tayar da fargaba a tsakanin al’ummomin da ke kusa da yankin, yayin da wasu mazauna garuruwan suka fara kaura zuwa wuraren da suke ganin sun fi tsaro.
A rahoton da ya wallafa a X, Zagazola Makama ya bayyana cewa rundunar sama ta Operation Fansan Yamma ce ta farmaki ‘yan bindiga da ke kokarin shiga jihar Kebbi daga jihar Zamfara, inda rahotanni suka ce an hallaka da dama daga cikinsu.
An gudanar da aikin ne a ranar 10 ga watan Agusta, bayan jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan yadda wata babbar kungiyar ‘yan bindiga ta fito daga yankin Sangeko Gap da ke Zamfara, tana matsawa zuwa Makuku a jihar Kebbi.
‘Yan bindiga 240 sun sha ruwan wuta
Majiyoyin tsaro sun ce adadin ‘yan bindigar ya kai kusan 240, inda suka rarrabu zuwa rukuni uku tare da amfani da babura wajen tafiya zuwa yankin da suke kokarin shiga.
Bayan samun bayanan sirrin, jami’an tsaro da suka hada da sojojin Najeriya da jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya suka fara tattara dakaru domin dakile ci gaban kungiyar.
Hakan ya kai ga barkewar kazamin artabu tsakanin jami’an tsaron da ‘yan bindigar yayin da suke kokarin dakile shigarsu cikin al’ummomin da ke yankin.

Source: Twitter
Rundunar NAF ta kai harin sama
Bayan fara artabun, jiragen rundunar sojin sama suka shiga aikin da wani hari na musamman daga sama domin dakile ci gaban ‘yan bindigar.
Majiyoyin da ke da masaniya kan aikin sun ce an kai harin ne kan wuraren da aka gano taruwar ‘yan bindigar, inda aka hallaka da dama daga cikin masu dauke da makaman.
Majiyoyin sun ce har yanzu ana ci gaba da tantance sakamakon harin domin gano cikakken adadin ‘yan bindigar da aka hallaka ko jikkata.
Sojoji sun ragargaji mayakan ISWAP
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta hallaka mayakan ISWAP tara, ciki har da wani babban kwamanda, a wani samamen sama a jihar Borno.
An gudanar da aikin ne ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2026, bayan samun bayanan sirri kan ayyuka da zirga-zirgar wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne a yankin dajin Sambisa.
Asali: Legit.ng
