Fadawa Tinubu 'Gaskiya' na Neman Jefa Malaman Addini a cikin Matsala

Fadawa Tinubu 'Gaskiya' na Neman Jefa Malaman Addini a cikin Matsala

  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya soki shugabannin Cocin Katolika kan sukar gwamnatin Bola Tinubu
  • Dare ya ce kalaman da limaman suka yi bayan ganawarsu da shugaban ƙasa sun yi kama da na 'yan adawa maimakon nasiha ta addini
  • Ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa sun ceci tarayyar Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Sunday Dare, ya mayar da martani kan kalaman da shugabannin Cocin Katolika suka yi bayan ganawarsu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dare ya zargi shugabannin KatoMalamilika, musamman John Cardinal Onaiyekan da shugaban taron Bishop-Bishop na Katolika na Najeriya (CBCN), Matthew Ndagoso, da yin kalaman da suka yi kama da na 'yan siyasa maimakon na shugabannin addini.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi ga yan Najeriya game da addininsu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da Bola Tinubu ya gana da limaman Katolika a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sunday Dare ya wallafa martanin da ya yi ne a wani sako da ya fitar a shafinsa na Facebook yayin da ake cigaba da takaddama kan batun.

Dare ya soki limaman Katolika

A cikin sakon da ya fitar, Sunday Dare ya ce Najeriya ta yi tsammanin shugabannin cocin za su gabatar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen tafiyar da ƙasa.

Sai dai ya ce, a maimakon haka, kalaman da suka fito daga gare su sun yi kama da sukar siyasa da kuma maimaita ra'ayoyin 'yan adawa.

Ya ce:

"Tasirin da limamin addini yake da shi yana fitowa ne daga kasancewarsa sama da bangaranci. Da zarar ya fara kama da ɗan siyasa, wannan tasiri yana raguwa."

Ya kuma soki Cardinal Onaiyekan saboda kalaman da ya yi bayan ganawar da suka yi da shugaban ƙasa, yana mai cewa ya kamata ya fara bayyana abin da shugaban ya faɗa kafin ya fassara shi ta ra'ayinsa.

Kara karanta wannan

Malami ya bankado 'sirrin' Tinubu game da neman cin zabe ta kowace hanya

Dare ya kare gwamnatin Tinubu

Sunday Dare ya ce Shugaba Tinubu ya karɓi mulki ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsanancin rikicin tattalin arziki da bashi.

Ya bayyana cewa cire tallafin man fetur, haɗa tsarin canjin kuɗin ƙasashen waje da sauran gyare-gyaren tattalin arziki sun taimaka wajen dawo da daidaito ga tattalin arzikin ƙasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu na jawabi a wajen wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewarsa, gwamnatin ta ƙaddamar da shirin NELFUND domin taimaka wa ɗalibai, ta ƙara kuɗin da jihohi ke samu daga FAAC, tare da saka hannun jari a noma, matatun mai da manyan ayyukan more rayuwa.

Punch ta wallafa cewa ya yi watsi da zargin cewa gwamnatin Tinubu na shirin nuna ƙarfin iko a zaɓen 2027, yana mai cewa shugaban ƙasar yana da tarihin gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya.

Soyinka ya soki Bola Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen marubuci kuma wanda ya lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya cika alƙawarinsa na sake duba fayel din kashe-kashe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Obasanjo gori, ya tabo batun hana tsohon shugaban wa'adi na 3

Soyinka ya kuma bukaci gwamnatin tarayya kada ta yi shiru kan kisan Deborah Samuel, ɗalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da aka kashe bayan zargin yin batanci.

Ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar an hukunta duk masu hannu a irin waɗannan kashe-kashe domin dawo da amincewar jama'a ga tsarin shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng