An Samu Afkuwar Ambaliya a Arewa, Gidaje da Wasu Muhimman Kadarori Sun Lalace
- Ambaliyar ruwa ta lalata kadarori da dama da darajarsu ta kai miliyoyin Naira a wani sashe na Gidan Gwamnatin Mohammed Inuwa Wushishi da ke Minna
- Mazauna yankin sun ce ambaliyar ta mamaye gidaje tare da lalata abinci, takardu, katifu, dabbobi da sauran kadarori
- Hukumar NSEMA ta buƙaci mazauna yankunan da ke kusa da magudanan ruwa da koguna su koma wurare masu tsaro da tudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Neja – Ambaliyar ruwa ta lalata kadarori da dama da darajarsu ta kai miliyoyin Naira tare da mamaye wasu gidaje a wani sashe na sanannen rukunin gidajen Janar M.I. Wushishi da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.
Lamarin ya sa wasu mazauna yankin suka fice daga gidajensu yayin da ruwa ya mamaye gidaje da dama.

Source: Facebook
Ambaliyar ruwa ta yi barna a Niger

Kara karanta wannan
Fitattun 'yan TikTok 3 sun fara ganin sakamako bayan sun taɓa mutuncin shugaban ƙasa
An ga mazauna yankin suna ƙoƙarin kwashe kayayyakin da suka rage daga gidajensu domin ceto abin da za su iya bayan ambaliyar, in ji rahoton Channels TV.
Waɗanda lamarin ya shafa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta shiga tsakani tare da magance matsalar ambaliyar da kuma abubuwan da ke haddasa ta a yankin.
Ɗaya daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa, Waziri Ahmed, ya ce ruwa ya lalata kusan dukkan abubuwan da ke cikin gidansa.
Ya ce daga cikin abubuwan da ambaliyar ta lalata akwai kayan abinci, takardu, katifu da dabbobi.
Ahmed ya bayyana cewa ruwan ya kai tsayin ƙirjinsa, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin fitar da yaransu zuwa wuraren da suka fi tsaro.
Ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa iyalan da abin ya shafa, musamman ganin cewa da dama daga cikinsu sun rasa muhimman kadarori da hanyoyin samun abin dogaro.
Wata mazauniyar yankin, Bamidele Ajayi, ita ma ta ce ruwa ya cika gidanta tare da kwashe motarta da kusan dukkan abubuwan da take da su.
An alakanta ambaliyar da ma'adinai
Ajayi ta ce an sanar da mazauna cewa ayyukan haƙar ma'adanai ne suka toshe hanyar da ruwa yake bi a zahiri, wanda hakan ya sa ruwan ya dawo ya mamaye wuraren da ake zaune.
Ta buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin magance matsalar tare da taimaka wa mutanen da ambaliyar ta shafa.
Ajayi ta kuma nuna damuwa kan yadda aka dade ana samun alkawuran gwamnati na magance matsalar, amma ba a samu ɗorewar mafita ga yawan ambaliyar da ke faruwa ba.
Ko da yake ba a samu rahoton asarar rai a wannan sabon lamarin ba, mazauna yankin sun buƙaci a gaggauta gyara magudanan ruwa da aka toshe tare da farfaɗo da hanyoyin fitar da ruwa.
Sun kuma yi kira da a sanya ido kan ayyukan da ka iya ƙara jawo ambaliya yayin da ake shiga tsakiyar daminar bana.
NSEMA ta yi gargaɗi
A nata ɓangaren, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta buƙaci mazauna yankunan da ke kusa da magudanan ruwa, hanyoyin ruwa da gabar koguna su koma wurare masu tsaro da tudu.
Daraktan Agaji da Farfaɗowa na hukumar, Yusuf Mohammed, ya bayyana hakan ne yayin da yake duba girman barnar da ambaliyar ta haddasa.

Kara karanta wannan
Kano: Halin da kadarorin Malami ke ciki bayan kotu ta kwace su saboda almundahana
Mohammed ya bayyana lamarin a matsayin ambaliyar bazata da ta afku tun kafin lokacin da ake yawan tsammanin samun ambaliyar ruwa mai tsanani a jihar.
Ya ce hukumomin hasashen yanayi da ambaliyar ruwa daban-daban sun riga sun gargadi jihar kan yiwuwar samun ruwan sama mai yawa da ambaliyar ruwa a bana.
Daga cikin gargadin akwai hasashen yanayin damina da kuma hasashen ambaliyar ruwa na shekara.
Asali: Legit.ng
