Mayakan ISWAP Sun Sha Wuta, an Hallaka Babban Kwamanda Mai Hatsari

Mayakan ISWAP Sun Sha Wuta, an Hallaka Babban Kwamanda Mai Hatsari

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta hallaka mayakan ISWAP tara, ciki har da wani babban kwamanda, a wani samamen sama a jihar Borno
  • An kai samamen ne ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, bayan samun bayanan sirri kan motsin ’yan ta’addan a yankin dajin Sambisa
  • NAF ta ce mutuwar kwamandan na iya kawo cikas ga zirga-zirgar manyan ’yan kungiyar da tsarin tsaron su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin labarai, siyasa da al'amuran yau da kullum, wanda ke da gogewa wajen nazarin al'amuran da suka shafi Najeriya

Jihar Borno - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta hallaka mayakan Islamic State West Africa Province (ISWAP) tara, ciki har da wani babban kwamanda, a wani samamen sama da ta kai a jihar Borno.

An gudanar da aikin ne ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2026, bayan samun bayanan sirri kan ayyuka da zirga-zirgar wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne a yankin dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Sakon Abba ga Malamai, Sarakuna da Gwamnonin da suka halarci auren gata a Kano

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Punch ta ce Air Commodore Ehimen Ejodame, daraktan hulda da jama’a da yada bayanai na NAF, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2026.

Yadda aka kashe mayakan ISWAP

Ejodame ya ce an fara aikin ne bayan tura wani jirgin sama mai sarrafa kansa daga nesa (RPA) domin gudanar da aikin leken asiri, sa ido da bincike (ISR) a kai a kai.

Ya ce hakan ya bai wa rundunar damar bin diddigin wasu ’yan ta’adda da ke tafiya zuwa wani wurin da ake zargin maboyarsu ne.

Bayan an tabbatar da ainihin inda aka nufa, jirgin ya kai wani samame na musamman kan wurin.

“Binciken illar da aka yi wa wurin daga baya ya nuna cewa an samu gagarumin tasiri a sansanin da aka nufa, inda aka hallaka wasu ’yan ta’adda,” in ji shi.

Sojojin sama sun samu nasara kan ISWAP

Kara karanta wannan

Ana dab da zaben gwamna, 'yan sanda sun cafke kwamishina a jihar Osun

A cewar Ejodame, karin bayanan sirri da aka samu bayan aikin sun tabbatar da cewa an hallaka mayakan ISWAP tara, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Daga cikin wadanda aka ruwaito an hallaka akwai Abu Khalid Al Muhajir, wanda NAF ta bayyana a matsayin kwamandan ISWAP mai kula da samar da rakiyar tsaro ga manyan jami’an kungiyar yayin da suke tafiya.

Rundunar ta ce ana sa ran mutuwarsa za ta shafi yadda kungiyar ke gudanar da zirga-zirga da kuma tsarin kare manyan jami’anta, musamman saboda rahotannin da ke nuna cewa ya san hanyoyi da yanayin wuraren da ke hada maboyar ’yan ta’adda a dajin Sambisa da yankunan da ke kewaye.

Ejodame ya ce bayanan sirri sun kuma nuna cewa wasu daga cikin ’yan ta’addan da samamen ya rutsa da su na da alaka da wasu da ake zargi da hannu a kwanton baunar da aka yi wa sojojin Najeriya a baya-bayan nan a kan hanyar Bita-Yamtage a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Ana samun nasara kan 'yan ta'adda

Ya ce aikin ya nuna yadda ayyukan sojin sama da ake jagoranta bisa bayanan sirri ke kara samun tasiri, musamman amfani da sa ido a kai a kai da kuma kai hare-haren da aka tsara daidai domin gano tare da kai wa ’yan ta’adda hari.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

NAF ta ce ana kuma sa ran aikin zai kawo cikas ga zirga-zirgar manyan ’yan ISWAP da kuma yadda suke tsara ayyukansu a maboyar kungiyar daban-daban.

Ejodame ya tabbatar da cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta ci gaba da gudanar da ayyukan sama bisa bayanan sirri tare da hadin gwiwar dakarun kasa domin rage karfin ’yan ta’adda, takaita ’yancin zirga-zirgarsu da kuma inganta tsaro ga al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a Arewa maso Gabas.

Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan ISWAP
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Boko Haram da ISWAP sun gwabza fada

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani sabon mummunan rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin Boko Haram masu gaba da juna a jihar Borno.

Fadan ya barke ne bayan mayaƙan Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun kai wani harin kwanton bauna kan mayaƙan Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad (JAS).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com