"Za Ka Sha Kaye"; Dan Takarar ADC Ya Yi Wa Gwamna Abba Barazana kan 2027
- Ibrahim Alamin Little da ke takarar gwamnan jihar Kano a inuwar jam'iyyar ADC, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sha kaye a zaɓen 2027
- Ɗan takarar na ADC ya kuma bayyana Abdulkadir Shehu Bari a matsayin abokin takararsa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Ibrahim Alamin Little ya yi alƙawarin mayar da hankali kan ilimi, lafiya da bunƙasa matasa idan ya samu damar zama gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano – Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Kano, Alhaji Ibrahim Alamin Little, ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Alhaji Ibrahim Alamin Little ya gargadi Gwamna Abba da ya shirya barin gidan gwamnati, yana hasashen cewa zai sha kaye a zaɓen gwamna na 2027.

Source: Facebook
Little ya bayyana haka ne a Kano yayin wani taron manema labarai, inda ya sanar da Abdulkadir Shehu Bari daga ƙaramar hukumar Rogo a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan
2027: Matawalle ya fito fili ya bayyana irin zaben da za a yi karkashin gwamnatin Tinubu
Ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da gudanar da ayyuka ta hanyar abin da ya kira “window dressing”, yana mai cewa al’ummar jihar na buƙatar gwamnati mai iya magance matsalolin da suke fuskanta.
A cewarsa, masu zaɓe za su cire gwamnatin mai ci daga mulki a 2027 saboda ƙara nuna damuwa kan matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ilimi, kiwon lafiya da fannin noma.
Little ya soki gwamnatin Kano
Little ya nuna damuwa musamman kan ƙaruwa da ake samu na matasan da ke safarar miyagun ƙwayoyi da kuma shaye-shayensu, yana mai bayyana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da jihar ke fuskanta.
Ya kuma soki gwamnatin kan abin da ya bayyana a matsayin rashin isasshen kulawa ga ilimi da kiwon lafiya, da kuma ƙarancin tallafin da ake bai wa manoma.
Ɗan takarar na ADC ya ce noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Kano, amma ya ce manoma na buƙatar samun takin zamani, kayan aiki da sauran abubuwan da ake amfani da su wajen noma cikin sauƙi domin ƙara yawan amfanin gona.
Dan takarar ADC ya yi alkawura
Little ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa matasa da kuma ƙarfafa mata.
Ya kuma yi alƙawarin magance matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi tare da samar da shirye-shiryen jin daɗin jama’a ga masu rauni, ciki har da zawarawa, marayu da yaran da ba sa zuwa makaranta.
"Da zarar an shigar da mu gidan gwamnatin Kano bayan zaɓen 2027, za mu tabbatar mun magance matsalolin da suka addabi ɓangaren kiwon lafiya tare da samar da ingantattun shirye-shiryen jin daɗin jama’a ga masu rauni a cikin al’umma.” In ji shi.

Source: Facebook
Ya yi alƙawarin sauya tsarin mulki
Little ya ƙara yin alƙawarin sake fasalin tsarin gudanar da gwamnati baki ɗaya domin tabbatar da samun dama iri ɗaya ga ’yan ƙasa ba tare da la’akari da matsayinsu ko asalinsu ba.
Ya ce gwamnatinsa za ta bunƙasa kirkire-kirkire da harkokin kasuwanci ta hanyar kafa cibiyoyin tattalin arziki a sassa daban-daban.
A cewarsa, shirin zai taimaka wajen sauya Kano daga al’ummar da ta fi dogaro da saye da amfani da kayayyaki zuwa tattalin arziki mai samar da kayayyaki, wanda zai samar da ayyukan yi, ƙara arziki da kuma inganta rayuwar mazauna jihar.
An karrama Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar mata yan jarida ta Najeriya (NAWOJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari.
Bayanai sun nuna cewa an ba gwamnan lambar yabon ne saboda irin ci gaban da gwamnatin sa ke samarwa a jihar Kano daga watan Mayun 2023.
Asali: Legit.ng

