NDC: Jam'iyyar Su Kwankwaso Ta Fitar da Kudin Fom din Takarar 2027

NDC: Jam'iyyar Su Kwankwaso Ta Fitar da Kudin Fom din Takarar 2027

  • Jam'iyyar adawa ta NDC ta fitar da kudin fom domin masu son shiga takara a matakai daban-daban da suke so a fafata da su a 2027 su saya
  • Shugabannin jam'iyyar NDC sun bayyana cewa kudin fom din sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa zai kasance a kan Naira miliyan 60
  • A 'yan kwanakin nan ne tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi suka koma NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar NDC ta fitar da jadawalin sayar da fom, tantance masu neman takara da kuma zaɓen fidda gwani gabanin zaɓen shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne bayan gudanar da babban taron jam'iyya na kasa a makon da ya wuce da ya samu halartar Rabiu Kwankwaso da Peter Obi a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Sabani ya bulla APC bayan kifar da mutum 150 yayin tantance masu son takara

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
Peter Obi na magana da Rabiu Kwankwaso a wajen taron NDC. Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da NDC ta yi game da kudin fom, zaben fitar da gwani da sauransu a wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X.

2027: Kudin fom din NDC

Jam’iyyar ta sanya kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa a kan Naira miliyan 60 — wanda ya ƙunshi Naira miliyan 20 na fom ɗin nuna sha’awa da kuma Naira miliyan 40 na fom ɗin tsayawa takara.

Jam’iyyar ta kuma sanar da cewa kuɗin fom ɗin gwamna zai kai Naira miliyan 30, wanda ya haɗa da Naira miliyan 10 na fom ɗin nuna sha’awa da kuma Naira miliyan 20 na fom ɗin tsayawa takara.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa fom ɗin takarar Sanata zai kai Naira miliyan 8, yayin da na Majalisar Wakilai zai kai Naira miliyan 6, sannan na Majalisar Dokokin Jiha zai kai Naira miliyan 2.5.

Yaushe za a fara sayar da fom?

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Jam’iyyar NDC ta ce za a fara sayar da fom ɗin ranar Laraba, 13 ga Mayu, 2026, kuma za a rufe ranar Litinin, 18 ga Mayu, 2026.

Bisa jadawalin, tantancewa da hira da masu neman takara zai gudana daga Talata, 19 ga Mayu zuwa Alhamis, 21 ga Mayu, 2026.

Punch ta rahoto cewa jam’iyyar ta shawarci duk masu neman takara da su halarci aikin tantancewar tare da takardunsu da sauran muhimman bayanai.

Yan NDC a wajen taro A Abuja
Lokacin da NDC ta yi babban taronta na kasa a Abuja. Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

An tsara gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ranar 29 ga Mayu, 2026 a Abuja. Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnoni a matakin ƙananan hukumomi.

Rudani kan tantance 'yan APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa an samu sabani bayan kwamitin tantance masu neman shiga takara na APC ya kayar sama da mutum 150.

Wasu daga cikin wandanda ba su tsallake tantancewa ba sun sauya sheka, wasu kuma sun yi barazanar zuwa kotu kan cewa an danne hakkinsu.

Wasu 'yan jam'iyyar APC a Taraba, Kano, Benue, Jigawa da sauran jihohi sun nuna fushi kan hana su damar tsayawa takara a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng