Jami'in Gwamnatin Tinubu Ya Goyi Bayan Takarar Pantami a Gombe

Jami'in Gwamnatin Tinubu Ya Goyi Bayan Takarar Pantami a Gombe

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma ambasadan Najeriya a Afrika ta Kudu, Femi Fani-Kayode ya yi magana kan siyasar jihar Gombe
  • Femi Fani-Kayode ya nuna goyon baya ga Sheikh Isa Ali Pantami, inda ya yi fatan ya samu tikitin APC domin mata takarar gwamna a 2027
  • A ranar Laraba, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi zama da jami'an tsaro domin tabbatar da an yi zaben fitar da gwani cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Siyasar jihar Gombe na cigaba da daukar hankali bayan hira da 'yan jarida da daya daga cikin masu neman takara, Sheikh Isa Ali Pantami ke yi.

Ambasadan Najeriya a Afrika ta Kudu, Femi Fani-Kayode ya bayyana goyon bayan shi ga Sheikh Isa Ali Pantami da ke fatan zama gwamna a Gombe.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Femi Fani-Kayode da Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a hagu, Femi Fani-Kayode a dama. Hoto: Professor Isa Ali Pantami|Femi Fani-Kayode
Source: Facebook

Fani-Kayode ya yabi Pantami

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa Sheikh Isa Ali Pantami mutumin kwarai ne da ya ke fatan ya zama gwamna a Gombe.

Ya ce:

"Ina yi wa babban abokina kuma ɗan’uwana Sheikh (Farfesa) Isa Ali Pantami, tsohon ministan sadarwa, fatan alheri a zaɓen fidda gwani na gwamna a jihar Gombe.
"Ina fatan ya samu tikitin takara, ya ɗaga tutar jam’iyyarmu kuma ya ci zaɓen. Abin alfahari ne ga Najeriya kuma zai zama gwamna nagari. Allah Ya yi masa jagora, Ya ba shi nasara."

Shirye-shiryen zaɓen fidda gwani

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya jagoranci taron majalisar tsaro ta jihar gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyu da za a yi.

Mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa Inuwa ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi fatali da buƙatar malaman addini, ya ƙi kashe masu kudin al'umma

Ya kara da cewa an yi zaman ne:

"Domin tabbatar da gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa cikin lumana ba tare da wata matsala ba a faɗin jihar."

Babban taron tsaron ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro da sauran muhimman masu ruwa da tsaki domin nazarin halin tsaro da tsara hanyoyin tabbatar da doka da oda.

Gwamna Inuwa Yahaya da jami'an tsaro a Gombe
Gwamnan Gombe yayin zama da jami'an tsaro gabanin zaben fitar da gwani. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Batun zaman lafiya a Gombe

Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada cewa dole ne a kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin da aka samu a jihar Gombe ko ta halin ƙaƙa.

Ya kuma buƙaci ’yan siyasa, magoya bayan jam’iyyu da mazauna jihar su gudanar da lamuransu cikin lumana da ɗa’a ga doka da oda.

Pantami ya ce ya cancanta

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya cancanci zama dan takarar jam'iyyar APC a jihar Gombe.

Malamin ya fadi abubuwa hudu da ya ce su suka bambanta shi da sauran 'yan siyasar jihar da ke neman tikitin takarar gwamna a karkashin APC.

Ya bayyana haka ne bayan gwamna Inuwa Yahaya ya nuna goyon baya ga Jamilu Isiyaku Gwamna maimakon Pantami ko Saidu Ahmed Alkali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng