Sabon Rashin Mutunci: 'Yan Bindiga Sun Kakabawa Manomi Haraji kafin Girbi

Sabon Rashin Mutunci: 'Yan Bindiga Sun Kakabawa Manomi Haraji kafin Girbi

  • 'Yan bindiga a jihar Benue sun nemi wani manomi da ya biya su kuɗi N500,000 kafin ya sami damar shiga gonarsa domin girbe amfani
  • Matakin na zuwa ne a yayin da 'yan bindiga ke ci gaba da addabar mutanen ƙauyen Mbagena da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala tare da daurawa manoma haraji
  • Ɗan manomin, John James, shi ne ya tonawa 'yan bindigar asiri yayin wani taron bita da kungiyar SERAP ta shirya a garin Makurdi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue – Wani manomi a ƙaramar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue ya tsere daga muhallinsa sakamakon matsin lamba da barazana daga 'yan bindiga wadanda suka nemi ya biya su N500,000.

Manomin, wanda mazaunin gundumar Mbagena ne, ya shiga wannan halin ne sakamakon ƙaruwar ayyukan 'yan bindiga da suke karɓar haraji da kuɗin amfanin gona daga hannun mazauna yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da manoma, sun bukaci N100m

Taswirar jihar Benue
Taswirar jihar Benue a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Vnaguard ta wallafa cewa dan manomin, John James ya bayyana wannan abun takaici a ƙarshen mako yayin wani taron bita kan haƙƙoƙi da tsaro da ƙungiyar SERAP ta shirya a Makurdi.

'Yan bindiga sun sa haraji

James ya bayyana cewa mahaifinsa, wanda yake haɗa aikin gwamnati da na gona, ya fada hannun 'yan bindigar ne tsawon sati biyu da suka gabata da suka kutsa gidansa da daddare suna neman N500,000.

A cewarsa, 'yan bindigar sun fara ba shi wa'adin kwana uku ne kawai, amma daga baya suka ƙara masa wa'adin zuwa mako guda bayan ya bayyana musu cewa ba shi da kuɗi a hannu har sai ya girbe amfanin gonarsa na gyaɗa, riɗi, da waken soya.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce:

"Kimanin mako biyu da suka gabata, tsagerun sun mamaye mahaɗar gidanmu da daddare yayin da yake barci tare da mahaifiyata.

Kara karanta wannan

"Mun bar ku da Allah': Mazauna Sokoto sun tura sako ga Gwamna kan rashin tsaro

'Sun buƙaci ya biya su N500,000 matsayin kuɗin fansa. Mahaifina ya roƙe su saboda babu kuɗi a lokacin, kuma ya yi hakan ne domin tsira da rayuwarmu saboda tuntuɓar jami'an tsaro zai ƙara tsananta al'amari."

An sace matar manomi a Benue

Yayin da mahaifin yake ƙoƙarin tara kuɗin, 'yan bindigar sun sake komawa gidan inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa saboda zargin jinkirin biyan kuɗin.

An saki mahaifiyar daga baya sakamakon firgici da halin ƙuncin da ta shiga, amma an lallasa ta tare da yi mata azaba mai tsanani.

Daga karshe, mahaifin ya tara N200,000 ta hanyar taimakon abokai da 'yan uwa, inda ya mika wa 'yan bindigar a tsakiyar daren ranar Alhamis.

Tunda kuɗin bai cika ba, 'yan bindigar sun amince ya girbe ɓangare guda kawai na amfanin gonar, inda suka kafe a kan cewa lallai sai ya biya sauran N300,000 kafin ya kammala girbe sauran amfanin gonar.

Wasu mutane a hanyar gona
Yadda wasu jama'a ke kan hanyar zuwa gona aiki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A halin yanzu, Barazanar 'yan bindigar ta sanya mahaifin gudu daga garin inda ya bar amfanin gonar tasa.

NCS ta kama makamai a Legas

A wani labarin dabam, mun ruwaito cewa hukumar NCS ta sanar da kammala bincike da sarrafa manyan makaman da ta kama a Legas.

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Kakakin rundunar ta NCS, Abdullah Maiwada, a ranar Lahadi ya bayyana matakin a matsayin wani babban mataki na dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar.

Wannan sanarwa ta biyo bayan abin da Shugaban Hukumar Kwastam na Ƙasa, Adewale Adeniyi, ya fitar inda ya bayyana cewa sun kama makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng