Sanatan APC Ya Fadi Yadda Atiku ke Rage Masu Wahala a Zaben 2027

Sanatan APC Ya Fadi Yadda Atiku ke Rage Masu Wahala a Zaben 2027

  • Adams Oshiomhole ya bayyana cewa rabuwar kai tsakanin shugabannin adawa na ƙara ƙarfafa jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen 2027
  • Sanatan mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce jagoran ADC, Atiku Abubakar, ya zama jagoran yaƙin neman zaɓen APC ba tare da ya sani ba
  • A cewar Oshiomhole, Atiku da magoya bayansa sun fara kai wa Peter Obi hari tun bayan da tsohon gwamnan jihar Anambra ya bar ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja — Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole ya ce rabuwar kai tsakanin shugabannin jam’iyyun adawa za ta sa APC ta samu sauƙin ci gaba da riƙe mulki a zaɓen 2027.

Ya bayyana haka ne bayan samun sabanin da ya kai ga sauya jam'iyya tsakanin su Atiku Abubakar da bangaren Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito da korafe korafe kan Buhari game da taimaka masa a 2015

Adams Oshiomhole da Atiku Abubakar
Sanata Adams Oshiomhole a hagu, Atiku Abubakar a dama. Hoto: Paul O Ibe|Adams Oshiomhole
Source: Facebook

Da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television ranar Laraba, Oshiomhole ya ce Atiku Abubakar ya zama manajan yaƙin neman zaɓen APC saboda hare-haren da yake kai wa Peter Obi.

Adams Oshiomhole ya yi ba’a ga ’yan adawa

A cewar Oshiomhole, Peter Obi da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, su ma suna kai wa juna hari, abin da tsohon gwamnan jihar Edo ya ce zai amfani APC a 2027.

Legit.ng ta rawaito cewa Atiku Abuabakar da Rotimi Amaechi dukkansu jiga-jigan jam'iyyar adawa ta ADC yayin da Peter Obi ke NDC.

Oshiomhole ya ce:

“Kana nufin APC za ta damu da wata jam’iyya a yanzu… ADC?
"Atiku ne yanzu babban manajan yaƙin neman zaɓenmu saboda yana kai wa Obi hari, sannan ina ganin Obi yana kai wa Amaechi hari.
"Ga kuma Amaechi yana cewa Obi ɗan siyasa ne maras karbuwa a wasu yankuna, haka zalika Atiku ma, shi kaɗai ne ɗan siyasar da ya samu karbuwa a ƙasa baki ɗaya, amma bai gaya mana yadda mazabarsa take ba.”

Kara karanta wannan

Duk da yana NDC, Kwankwaso ya tabo batun aiki tare da Atiku, ADC a 2027

Oshiomhole yana ganin nasarar Bola Tinubu

Bugu da ƙari, The Sun ta rahoto Sanatan ya nuna ƙwarin gwiwar cewa za a murƙushe ’yan adawa a zaɓen 2027, komai irin shirin haɗakar siyasar da suke yi.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tsohon gwamnan mai shekara 74 ya ƙalubalanci shugabannin adawa da su gaya wa ’yan Nijeriya abin da za su yi daban da manufofin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa yanzu.

Ya ce:

“’Yan adawa za su iya cika baki, amma za a doke su ƙasa warwas saboda babu wanda ya yarda da su.
"Dole su bayyana wa mutane sababbin manufofin da za su kawo, ko za su dawo da tsohon tsarin haraji, ko dawo da tallafin mai, ko soke bashin karatun ɗalibai, ko kuma su soke wasu daga cikin ƙwararan matakan da Shugaba Tinubu ya ɗauka.”

An samu sabani cikin jam'iyyar APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa shirin tantance 'yan takara da APC ta yi bayan sayar da fom ya jefa rudani a tsakanin mambobin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

2027: Yadda 'yar Kwankwaso ta shawo kan shi game da hada kai da Obi

Wani bincike ya nuna cewa sama da mutum 150 ne suka gaza tsallake ka'idojin tantancewa da APC ta gindaya, lamarin da bai yi wa wasu dadi ba.

Wasu daga cikin 'yan APC a Taraba, Gombe, Kano, Yobe da sauransu sun ki amincewa da 'yar takarar da jam'iyyar ta zaba ta hanyar yarjejeniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng