ADC Ta Kasa Sasanta Rikicinta a Katsina, Manyan Jiga Jigai 2 Sun Fice daga Cikinta

ADC Ta Kasa Sasanta Rikicinta a Katsina, Manyan Jiga Jigai 2 Sun Fice daga Cikinta

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a jihar Katsina ta yi babban rashi bayan wasu manyan jiga-jiganta sun raba gari da ita
  • Tsohon Darakta-Janar na DSS, Lawal Musa Daura, ya yi murabus daga ADC tare da komawa jam'iyyar APM
  • Lawal Daura ya ce shirun da ya yi bayan rikicin ADC wani bangare ne na shirye-shiryensa na daukar matakin siyasa mafi dacewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Manyan ‘yan siyasar Katsina guda biyu da suka nemi tikitin takarar gwamna a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sun yi murabus daga jam’iyyar bayan sun sha kaye a zaben fidda gwani na gwamna a jihar.

‘Yan siyasar su ne tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina (SSG), Dr Mustapha Muhammad Inuwa, da tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (DSS), Lawal Musa Daura.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: INEC ta yi wa jam'iyyu adalci kan mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisa

Mustapha Inuwa ya fice daga ADC
Mustapha Inuwa na yaga katinsa na jam'iyyar ADC Hoto: Mobile Media Crew
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce bayan ficewarsu daga ADC, Inuwa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da Daura ya sanar da komawarsa jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Inuwa ya koma APC

Inuwa, wanda tsohon SSG ne kuma gogaggen dan siyasar Katsina, shi ne na farko da ya sanar da yin murabus daga ADC.

Ya taba rike mukamin kwamishinan ilimi daga 2003 zuwa 2006, kafin daga bisani ya zama SSG a lokacin gwamnatin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.

Haka kuma, Inuwa ya sake zama SSG a gwamnatin tsohon gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, inda ya rike mukamin daga 2015 zuwa 2022.

A shekarar 2022, Inuwa ya yi murabus daga mukaminsa na SSG domin neman tikitin takarar gwamna a APC, amma Gwamna Dikko Umar Radda ya kayar da shi a zaben fidda gwani.

Daga bisani ya bar APC ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). A shekarar 2025, Inuwa ya koma ADC, inda ya zama daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: APC ta ɗora sunayen yan takarar gwamna da mataimakansu a shafin INEC

A shekarar 2026 kuma ya sake neman tikitin takarar gwamnan Katsina, a wannan karon karkashin ADC.

Bayan zaben fidda gwani, Inuwa ya ki amincewa da tsarin da ya samar da Sanata Ahmad Babba Kaita a matsayin dan takarar gwamnan ADC.

Ya ci gaba da rike matsayinsa har zuwa ranar Lahadi, 9 ga watan Agusta, 2026, lokacin da ya sanar a hukumance cewa ya yi murabus daga ADC tare da komawa APC.

Daura ya koma APM

Shi ma Daura ya tsaya takarar tikitin gwamnan Katsina na ADC a shekarar 2026, amma Sanata Ahmad Babba Kaita ya kayar da shi.

Bayan kokarin sasanta shi da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar bai yi nasara ba, Daura ya sanar a hukumance cewa ya yi murabus daga ADC tare da komawa Allied Peoples Movement (APM).

Lawal Daura ya koma APM
Lawal Musa Daura zaune a kan kujera Hoto: Amb Abdul Kane Daura
Source: Facebook

Majiyoyi a cikin jam’iyyar sun bayyana cewa akwai yiwuwar a nada Daura a matsayin mataimakin Gwamna Seyi Makinde, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na APM.

Da yake magana a wani taro a Katsina, Daura ya ce shirun da ya yi bayan rikicin ADC wani bangare ne na shirye-shiryensa na abin da ya bayyana a matsayin zabin siyasa mafi inganci.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya jawo cece kuce bayan ya yi wasu kalamai

Ya bukaci magoya bayansa da su yi hakuri, yana mai cewa akwai sauran abubuwan da za su faru a karkashin sabuwar jam’iyyar tasu.

Sanata Onawo ya fice daga ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Mohammed Onawo, mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya fice daga jam’iyyar hadaka ta ADC) zuwa APM.

Sanatan ya kuma ya sanar da aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a zaɓen 2027 da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng